Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ba wani almajiri da ya kirkiri injin da za a rika amfani da shi a matsayin taraktar noma kyautar Naira miliyan biyar don kara karfafa wa masu hazaka irin tasa.
Almajirin, mai suna Laminu Muhammad dai ya yi amfani da sassan injin ban-ruwa ne, inda ya kera na’urar da za a iya yin noma da ita wacce ke aiki kamar tarakta da ake turawa da hannu.
- An kama tirela 2 makare da katan 2,000 na giya a Kano
- Yada bayanan ’yan ta’adda: Gwamnati za ta kafa wa BBC da Trust TV takunkumi
Laminu Mohammed mai shekara shekara 25 ya fito ne daga daga karamar hukumar Gubio da ke Arewacin jihar ta Borno.
Bayanai sun sunan almajirin bai taba zuwa wata makarantar boko ba, kuma bai san komai ba game da bokon.
Laminu dai ya yi amfani da sassan injin ban-ruwan samfurin Lister da aka kera tun asali don yin famfo ruwa, wajen kera na’urar da ke aiki kamar tarakta.
Gwamna Zulum, wanda Farfesa ne a fannin Aikin Noma, ya gayyaci Laminu, kuma a wata tattaunawa ta fasaha da Gwamnan, matashin ya nuna kwarewarsa wajen kera irin wannan na’ura.
Zulum ya ce kudaden na da nufin zaburar da ‘injiniya marar makaranta’ wajen samar da karin garma da al’ummar Borno za su amfana fiye da a baya.
Idan za a iya tunawa, Gwamna Zulum ya tallafa wa Laminu ne makonni biyu bayan ya amince da ba da makamanciyar wannan kyauta ga wani yaro mai shekara 13 da ke makarantar firamare da ya yi amfani da laka wajen zana gadar sama ta farko a Borno da ke Unguwar Kwastam a babban birnin jihar, wato Maiduguri.
A wani labarin kuma, Gwamnan ya bayar da kyautar kananan motocin bas guda biyar da tsabar kudi Naira miliyan 20 ga wani matashin dan jihar Borno da ya kware wajen mayar da motocin bas ma su aiki da man Fetur ya zuwa motocin masu amfani da hasken rana da lantarki.