Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce jihar karkashin jagorancinsa ta samu nasarar noma hekta 30,000 na shinkafa.
Zulum ya ce an samar da gonakin da aka fi noman ne a babban shirin gwamnatinsa na farfado da harkar noma.
- Muna shirin dawo da sufurin keke ka’in da na’in a Najeriya —FRSC
- ’Yan Najeriya na kewar mulkin PDP —Mu’azu Babangida
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, wanda ya kai ziyara daya daga cikin gonakin a ranar Laraba a Hedikwatar Karamar Hukumar Mobbar da ke jihar.
Zulum ya ce dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, ya sanya harkokin ban ruwa musamman a gonakin da ke kusa da Tabkin Chadi, Da dam din ruwa na Alau, da Baga, da Nguru Soye, da ma sauran gurare da dama a jihar sun dawo ka’in da na’in.
Haka kuma Zulum ya ce wannan cigaban ya sanya jihar ta dawo noman kayan lambu, madadin siyowa daga wasu jihohin Najeriyar da take a baya.
Da yake ganawa da manoman gwamna Bagudu na Kebbi da jiharsa tayi suna a noman shinkafar a Najeriya, ya ce ya rako Zulum Damasak ne domin ganewa idonsa dawowar ayyukan noma a jihar ta Borno.
“Da yake mana albishir da barun, sai na tambaye shi za ka tadi da ni rakiya zuwa Damasak? Domin kullum muna taya shi murna, da kuma yabawa da abinda yake a jihar Borno, da Najeriya baki daya”, in ji Bagudu.