✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ziyarar Kano

Wani Bakatsine ne da Bawuddire (mutumin Katagum) suka je Kano, inda suka kai ziyara gidan zu. Shigar su ke da wuya sai suka iske wani…

Wani Bakatsine ne da Bawuddire (mutumin Katagum) suka je Kano, inda suka kai ziyara gidan zu. Shigar su ke da wuya sai suka iske wani dawisu sai sheki yake. Bawuddire ya ce: “Gaskiya duk mai zanen da ya yi zane a jikin wannan dawisu, ba karamin mai basira ba ne. Bakatsine ya ce: “Ai ’yan birni za su yi ya fi haka.” Suna karawa gaba sai Bakatsine ya ga wata katuwar jimina sai ya ce: “Ah, Allah mai yadda Ya so, wannan kuma wani zakara ne ya samu wata ni’ima ya zama kato haka ko kuwa rakumi ne yunwa ta mayar da shi haka?”
Daga Isah Ramin Hudu, Hadeja 08060353382.