✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC

Jimullar waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar a wannan shekarar sun kai mutum 800.

Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce adadin mutanen da zazzaɓin lassa ya kashe bana sun kai 151 a fadin kasar.

Cikin wata sanarwa da NCDC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, ta ce yawan kisan da cutar zazzaɓin lassa ke yi ya ƙaru daga kashi 17.3 cikin 100 da aka samu a bara.

Sanarwar ta ce an yi bitar alkaluman mamatan a bana ne bisa  la’akari adadin waɗanda suka kamu kuma ta yi ajalinsu a shekarar 2024.

Hukumumar ta ce alkaluman mamatan ya kai kashi 18.9 cikin 100 na waɗanda suka kamu da ita a wannan shekara.

Sanarwar ta ce kwanan na an samu ƙarin mutum 11 da suka kamu da cutar a cikin jihohin ƙasar shida, lamarin da ya mayar da jimullar waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar a wannan shekarar mutum 800.

Kazalika, sanarwar ta ce kashi 90 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar suna cikin jihohin Ondo da Bauchi da Edo da Taraba da kuma Ebonyi ne.

Cutar zazzaɓin lassa dai tana yaɗuwa ne ta hanyar kashin ɓera, kuma cuta ce da ke iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum.