✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin tsafi da yarinya: Fasto da mabiyinsa sun sha da kyar a Abuja

Wani da aka bayyana a matsayin limamin coci a garin Tungan Maje da ke kusa da Zuba a Abuja, ya sha da kyar daga wajen…

Wani da aka bayyana a matsayin limamin coci a garin Tungan Maje da ke kusa da Zuba a Abuja, ya sha da kyar daga wajen wani gungun jama’a da suka auka masa tare da wani mabiyinsa, da ya gabatar masa da ’yarsa don yi mata magani ta hanyar sihiri.

Aminiya ta samu labarin cewa mutanen biyu sun dauki yarinyar ce tare da wasu abubuwa da ya hada da tukunyar laka da bakaken kyallaye, zuwa wata mahadar hanyar kafa, a gefen garin da misalign karfe 9 na daren Litinin da tagabata.

Bayanin ya nuna cewa fara aikin keda wuya, sai jama’a suka auka masu kan zargin suna shirin aikata tsafi ne da yarinyar, wacce ke da kamar shekara 6. Majiyar ta bayyana cewa, jama’ar sun jikkata faston kafin jami’an tsaron ’yan sanda da na ’yan banga suka kubutar da su, bayan labari ya kai gare su.

Da take zantawa da waklinmu, mahaifiyar yarinyar wadda ta ce ba ta wajen a farkon faruwan abin, ta ce ta yi ta rokon jama’ar tare da sanar da su cewa tana sane da zuwansu wajen tare da ’yar ta su, don faston ya yi mata magani.

“Ta ce daukan matakin yin maganin, ya biyo bayan mummunar mafarki ne da yarinyar ke yi, inda take ganin ana daure hannayenta da bakaken kyalle a kusa da tukunya, a waje da ke gefen gari. Bayan na sanar da fastonmu lamarin, sai ya bukaci da na tanadi kwatankwacin abubuwan don aikin kubutar da ita,” inji ta.

Shi ma a bayanin da ya yi, faston wanda ya bayyana sunan aikin nasa da “Sabatharian” ya ce yarinyar za ta warke daga matsalar mummunar mafarkin cikin sauki, inda ya ce a baya ya warkar da wasu da dama da matasalarsu ya dara na yarinyar, ta amfani da wannan hanyar.

Babban jami’in ’yan sanda na garin Zuba CSP Muhammad Yahaya ya ce bayan kai dauki ga mutanen biyu, sun kai faston zuwa wani asibti inda ya kwana a wajen, a yayin da suka garzayo da iyayen yarinyar zuwa ofishinsu don tsarewa da kuma ba su kariya. Ya ce za su sallame su da zarar hankali ya kwanta a yankin da suke da zama.