✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin ta’addanci: Yau gwamnati za a gurfanar da Tukur Mamu

Gwamnatin za ta gurfanar da shi ne a gaban kotun tarayya da ke Abuja kan zargin wasu laifuka masu nasaba da daukar nauyi da kuma…

A Talatar nan Gwamnatin Tarayya take gurfanar da Tukur Mamu, dan jaridar da ke tsare a hannun hukumar tsaro ta DSS kan zargin alaka da ’yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Gwamnatin za ta gurfanar da shi ne a gaban kotun tarayya da ke Abuja kan zargin wasu laifuka masu nasaba da daukar nauyi da kuma alaka da ’yan ta’adda.

A ranar 13 ga watan Janairu hukumar DSS ta samu umarnin ci ga da tsare Tukur Mamu na tsawon kwana 60 domin samun kammala bincike kan zargin da ake masa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Ministan Shari’a Abubakar Malami zai gurfanar da Mamu a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja.

Hukumar DSS ta tsare Tukur Mamu ne bayan zargin sa da karkatar da kudaden fansan da aka bai wa ‘yan bindiga; ya taka muhimmiyar rawa wajen tattaunawa da ’yan bindiga da kuma ganin an sako da dama daga cikin fasinjojin bayan iyalansu sun biya kudin fansa.

Jami’an tsaro sun fara tsare Mamu ne a kasar Masar, a lokacin da shi da iyalansa ke hanyarsu ta zuwa Umrah.

Daga bisani da aka taso keyarsu zuwa Najeriya, inda aka ci gaba da tsare shi da kuma gudanar da bincike a kansa.