Ministan Sadarwa na Najeriya, Isa Ali Pantami ya ba da wa’adin awa 24 ga kamfanin jaridar Daily Indpendent wadda ta wallafa labarin zarginsa da ayyukan ta’addanci da kuma kungiyar Boko Haram.
Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da labarin na Daily Independent ya tayar da kura musamman a kafafen sadar da zumunta, sannan daga baya ya bayyana cewa shaci-faci ne.
- Ba biyan albashi aka zabe ni in yi ba —El-Rufai
- Pantami zai maka kafar da ta zarge shi da ta’addanci a kotu
- An ga watan Ramadan a Saudiyya
A takardar da lauyoyinsa suka aike wa kamfanin, sun ba Daily Indepenent “Awa 24 ku janye labarin kuma ku wallafa a manyan jaridun Najeriya 5 da manyan kafafen intanet na duniya biyar, sannan ku kira taron ’yan jarida ku sanar da janye labarin, ku kuma nesanta wanda muke wakilta daga zargin da kuka yi.”
Wasikar ta ce, muddin ba a yi hakan ba cikin awa 24 da samun wasikar, kotu ce za ta raba su.
Ta bayyana cewa Pantami sanannen mutum ne kuma mai kima a idon duniya, wanda a matsayinsa na malami wanda ya wallafa litattafi masu dama a fadin duniya, labarin ya yi illa gare shi a idon duniya, musammana abokan huldarsa da mabiyansa da sauransu.
Tun da farko, binciken Aminiya ya gano cewa babu ko da kalmar Pantami, ballantana wani mutum mai suna Isa Ali, ko Isa Ibrahim, ko makamancin haka a cikin jerin mutanen da hukumar tsaro ta FBI ta Amurka take nema bisa zargin ta’addanci a cikin kasar ko a kasashen duniya.
Kazalika, babu wata babbar kafar yada labarai mai zaman kanta da ta ruwaito labarin da ya tayar da kura.
Muna nema afuwan Minista
Kafar NewswireNGR da ta ruwaito labarin daga Daily Independent ta janye labarin da ta wallafa tare da cewa, “Muna neman afuwar masu karatu saboda labarin da muka wallafa, muna kuma neman yafiyar Ministar Sadarwan Najeriya, Sheikh Isa Pantami.
“Mun gudanar da bincike mai zaman kansa a kan labarin [namu] kuma muka gano cewa ba daga hukumar Amurkan (ta FBI) da aka ruwaito ya fito ba.”
Za mu hadu a kotu —Pantami
Amma a sakon da ya wallafa a shafinsa, Pantami ya ce kotu ce za ta raba shi da NewswireNGR.
“Nan gaba za mu hadu da manyan masu wallafa labarin a gaban kotu kan cin mutuncin da suka yi min,” inji shi.
“Janyewar ba ta isa ba”
Tuni wasu ’yan Najeriya suka fara bayyana ra’ayoyinsu a kan lamarin, inda yawancinsu ke shawartar Ministan ya maka kafar newswire a kotu.
Hadimin Shugaban Kasa, kan kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad, ya ce, “@NewsWireNGR kun dauka cewa janye labarin da kuka yi ta isa ta gyara ta kuma dakatar da barnar da labarinku ya yi wa @DrIsPantami?”
Tsoho takwaransa na Gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai (Dawisu) ya ce, “@DrIsaPantami, don Allah kar ka amince da janyewar. Ka samu wani Babban Lauya Najeriya (SAN) mai rai da lafiya, ya maka su a kotu. Labarin ya riga ya karade kafafen sada zumunta, kuma sun riga sun bata maka suna; ya kamata a buga misali da wasu daga cikin kafafen intanet ’yan farfaganda.”
Neman zubar da kima ne —Uwa
Janyewar na zuwa ne a daidai lokacin da kakakin Ministan, Uwa Sulaiman, ta fitar da sanarwa cewa labarin ba shi da makama.
Ta ce hankali ba zai dauka ba a ce duk da irin ayyukan da Pantami yake yi na yaki da ta’addanci, a same shi da hannu a abin da ake zargin.
“Tsare-tsaren farko da ya kawo a matsayinsa na Minista sun hada da yin rajistar layukan waya da nufin dakile ayyukan ta’addanci, wanda ya taka burki ga yadda a baya ake sayarwa da kuma yin rajistar layukan waya barkatai.
“Hade layukan waya da lambar dan kasa ta NIN da ake yi a yanzu kuma, an bullo da shi ne domin tabbatar da ganin tsarin rajistan layin wayan ya yi karko.
“Saboda haka babu yadda za a yi duk mutum mai lissafi ya je ya wallafa irin wannan labarin,” inji ta.
Uwa, ta kuma yi waiwaye ga barazanar hallaka Pantami da shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi saboda tsarin rajistar da rufe layukan waya marasa rajista da Ministan ya kawo.
Ta ce, “Ko dai har an manta barazar da Shekau ya yi masa ne, bayan da Ministan ya birkita musu lissafi, suka kasa ci gaba da harkokinsu yadda suka saba?”
Ko kafin NewswireNGR ta janye labarin, Daily Independent da ta wallafa labarin da aka gano cewa shaci-fadi ne, ta ambato wani hadimin Pantami –wanda ba ta bayyana sunansa ba– yana karyata labarin a matsayin na kanzon kurege.
“Wannan yunkuri ne kawai na zubar da mutunci da cin zarafin addinin da akidar mutum. Babu wani abin da Gwamnatin Amurka take zargin sa da aikatawa,” inji hadimin Ministan cikin bacin rai.
Ita ma Uwa, ta bayyana wa Sashen Hausa na BBC cewa, “An buga labarin ne da zummar bata sunan ministan.
“Wasu mutane ne da suka rasa yadda za su bullo wa Pantami domin su muzanta shi – shi ne suka fake da kirkirar labarin.”
Ra’ayin Pantami ka ta’addanci
Tun kafin nada shi matsayin Minista, Pantami ya kasance shahararren mai wa’azin Musulunci ne, kuma mai farin jini.
Ya kuma dade yana caccakar ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram a yayin karatuttukansa.
A shekarun baya, ya taba yin wata zazzafar mukabala da shugaban kungiyar Boko Haram na farko, Muhammad Yusuf, wanda jami’an tsaro suka kasha, inda a mukabalar Pantami ya hana shi sakat da tambayoyi da kuma ruwan hujjjoji.
Bayan zamansa Minista, Pantami ya bullo da tsare-tsare da dama ta zummar dakile kafafen gudanarwa da kuma taimaka wa ayyukan ta’addanci.
Daga cikinsu akwai tsarin yi wa layukan waya rajista da kuma rufe layukan waya marasa cikakkiyar rajista.
Ya kuma bullo da tsarin hade lambar NIN da layukan waya wanda a halin yanzu a ke ci gaba da yi.
A shekarar 2020, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya da su hada kai da Ministan, domin dakile ayyukan ’yan bindiga da suka addabi yankin Arewa-maso-yammacin Najeriya.