✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin Ta’addanci: Kotu ta sallami Shugaban Miyetti Allah Bello Bodejo

Kotu ta sallami Bello Bodejo, ban an jane zargin sa da hannu a zargin ta'addanci.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamata a Abuja ta sallami Shugaban Kungiyar Miyetti Allah, Alhaji Bello Bodejo, wanda aka gurfanar kan zargin ta’addanci.

A ranar Talata Mai Shari’a Inyang Ekwo ya sallami Bello Bodejo bayan Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati ya janye tuhumar da ake masa.

Wakilin Ministan Shari’ar, Aderonke Imana, ne ya gabatar da bukatar gwamnati na janye tuhume-tuhume uku da ake wa Bello Bodejo.

Lauyan wanda ake kara, Ahmed Raji (SAN) bai kalubalanci rokon masu karar ba, sai dai ma ya gode musu bisa karimcin, sannan ya bukaci, “Mai girma alkali ya sallami wanda ke zargin.”

Wa ranar 22 ga Maris, 2022 ne aka fara gurfanar da Bello Bodejo kan zargin laifuka uku masu alaka da kafa wata haramtacciyar kungiyar ’yan sa-kai mai suna Kungiyar Zaman Lafiya a Jihar Nasarawa.

An gurfanar da shi ne bayan hukumar tsaron ta DIA ta kama shi kan kafa kungiyar mai dakaru 1,144 a cikin watan Janairu.

Bodejo dai ya musanta aikata laifi, yana mai cewa an kafa kungiyar ce da nufin taimakawa wajen yakar ayyukan ’yan bindiga da satar shanu da dangoginsu.