✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin sakin tsohon Kwamishinan da ya ‘kashe’ abokinsa ya jawo zanga-zanga a Bauchi

Ana zargin tsohon kwamishinan da kashe abokinsa da mota kan yaudarar 'yarsa.

Daruruwan mazauna unguwar Yelwa Labura da ke cikin birnin Bauchi sun tare hanyar Bauchi zuwa Tafawa Balewa domin nuna adawa da sakin wani da ake zargin ya kashe abokinsa, Adamu Babanta da motarsa. 

Aminiya ta tattaro cewa da misalin karfe 7:00 na safiyar Talata ce matasan suka tare babbar hanyar Bauchi zuwa Tafawa Balewa da ke kusa da Kwalejin Aikin Gona, lamarin da ya hana zirga-zirgar ababen hawa, inda daruruwan matafiya suka makale sama da sa’o’i biyu.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce an shawo kan lamarin, yayin da ta tura jami’an tsaron hadin gwiwa domin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Kakakin rundunar a jihar, SP Ahmed Mohammed Wakili ya ce, an sami rahoton faruwar hatsarin mota daga sashen Yelwa kai tsaye zuwa MTD domin gudanar da bincike mai zurfi kuma wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda a tsare.”

Wakil ya ce, “Wata Khadijah Adamu Babanta, ‘ya ga wani mai suna Mohammed Damina, Galadiman Dass, mai shekara 68 mazaunin Yelwa ne ya yaudare shi. Da Galadima ya yaudare ta, sai ta shaida wa mahaifinta, sannan ta gaya wa mahaifin cewa mutumin nan yana jiranta a gidan mai na Total.

“Mahaifin ya bi ta a baya zuwa wurin. Suna isa ne mahaifin, wanda ya rasu a yanzu, ya tunkari Galadima ta bangaren kofar shigar fasinja, suna cikin tattaunawa, Galadima ya debi motar a guje yayin da marigayin ke makale a jikin kofar motar har ya kai ga faduwa wanda aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jamia’r Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) don a duba lafiyarsa, amma likita ya tabbatar da rasuwarsa.

“Yau [Litinin] da misalin karfe 7:00 na safe wasu bata-gari sun fito kan tituna suna zanga-zanga, suna tunanin cewar an sako wanda ake zargin daga ofishin ‘yan sanda, wanda ba haka lamarin yake ba, har yanzu yana hannunmu.

“Da samun rahoton, Kwamishinan ‘Yan Sanda, Umar Sanda, ya ba da umarnin dukkan kwamandojin da ke karkashin jagorancin kwamandan yankin da su kai dauki yankin,” inji Kakakkin ‘yan sandan.