An gurfanar da tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU), Farfesa Ibrahim Garba, a kotu kan zargin karkatar da Naira biliyan daya.
Hukumar Yaki da masu karya tattalin arzikin kasa (EFCC) ce ta gurfanar da shi tare da tsohon ma’ajin jami’ar, Ibrahim Shehu Usman, a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna.
- Mutum 26 sun saye kadarorin Diezani da aka yi gwanjonsu
- Ba na cikin hayyacina lokacin da Ummita ta rasu —Dan China
EFCC ta gurfanar da su ne a gaban Mai Shari’a A.A kan zargin aikata laifuka takwas da suka shafi sata da kuma safarar haramtatunk kudade da awansu ya kai Naira biliyan daya.
Hukumar ta gurfanar da shi ne bayan shafe watanni ta gudanar da binciken kwakwaf kan takardar korafin da aka rubuta kan su biyun na karkatar da kudaden da aka ware domin aikin kwaskwarimar otel din Kongo Conference, Zariya.
EFCC ta ce binciken ya gano yadda wadanda ake zargin suka karkatar da sama da Naira biliyan daya daga asusun banki daban-daban na jami’ar, zuwa aljihunsu.