✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin luwadi ya sa an ki ba ni aure – Adam Zango

Fitaccen jarumin nan Adam A. Zango ya ce zargin luwadi da wasu ke yi masa ya janyo an ki bashi auren wata yarin da ya…

Fitaccen jarumin nan Adam A. Zango ya ce zargin luwadi da wasu ke yi masa ya janyo an ki bashi auren wata yarin da ya nema.

Jarumin wanda har ila yau mawaki ne ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da gidan rediyon BBC a ranar Litinin din da ta gabata.

Zango ya bayyana cewa zargin da aka rika yaya ta shi, ya sanya shi cikin bakin ciki da kuncin rayuwa.

“Idan kana neman abin da na tsana a rayuwata ta duniya, na ji kamar zan kashe ka shi ne ka ce ina luwadi. Wannan zargi har janyo wa ya yi aka hana ni auren da na nema. Wannan abu ya ishe ni har yana hana ni barci”. Inji shi.

Shi ya sa na dauki matakin wanke kaina ta hanyar yin rantsuwa da al’kur’ani cewa ban tada yin luwadi ba.

Ya dage a kan cewa rantsuwar da ya yi za ta sanya wadanda ke yada jita-jitar su daina kuma za ta wanke shi a idon duniya.

Da aka tambaye shi ko akwai rashin jituwa a tsakaninsa da jarumi Ali Nuhu, sai ya ce Ali Nuhu Maigidansa ne wanda ba zai manta da shi a rayuwarsa ba.

Ya dage a kan cewa rashin jituwarsu ta samo asali ne daga matsalar da ya samu da jaruma Rahama Sadau.

Ya bayyana cewa goyon bayan Rahama Sadau da Ali Nuhu ya yi shi ne makasudin da ya rura wutar takun sakar da ta shiga tsakaninsu.

Ya bayyana cewa ya dauki kudurin komawa karatu har sai ya zama gwani a Harshen Turanci ta yadda zai iya yinsa a gaban jama’a ba tare da wata matsala ba.

Ya kara da cewa tuni har ya yi nisa wajen daukar darussa don cimma burin da ya sa a gaba a samun ingantaccen ilimi.

Kuma ya ce nan ba da jimawa ba jama’a za su sami labarin ya koma karatu gadan-gadan.

Ya bayyana cewa nan gaba ta iya yiwuwa ya jingine harkar fim da waka ya koma karatu baki daya.

Ya gasgata alakar soyayya da ke tsakaninsa da Nafisa Abdullahi amma ya dage akan cewa bai yaudare ta ba.

Ya bayyana cewa Allah ne bai kaddara aure tsakaninsa da jaruma Nafisa Abdullahi.