Zargin cogen shekaru ya mamaye gasar kwallon kwando da kamfanin Milo ya shirya wa makarantun sakandire da ke Jihar Kano.
Batutuwa kan zarge-zargen cogen shekarun ’yan wasa har ma da rashin kyakkyawan shiri ya ci gaba da mamaye gasar karo na 22 na shiyyar Jihohin Arewa da ake wa lakabi da Savanah conference da ake gudanarwa a Jihar.
- Dalibai sun kashe matashiya a Sakkwato saboda zargin batanci ga Annabi
- Kurunkus! Jonathan ya koma APC
A zantawar mu da wani babban mai ruwa da tsaki a gasar a rufaffen dakin wasanni na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano ranar Talata, lokacin da ake tsaka da gasar, ya nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya bayyana a matsayin rashin daidaito.
Sai dai binciken da muka yi ya gano cewa korafe-korafen magudin shekaru ya kasance fiye da kima sannan ya kawo cikas ga gasar da ta dalibai ce.
Jihohin da ke fafatawa na ci gaba da musayar zarge-zargen cogen shekaru ga junansu.
Wani mai horar da ’yan wasan kwallon kwando da ke da alaka da daya daga cikin ’yan wasan ya koka da cewa “Wannan ita ce gasar Milo mafi muni da aka taba gudanarwa.
“Masu shirya gasar sun yi ta mara kyau, sun gudanar da tantancewa, wasu ’yan wasan sun wuce shekaru, amma abin mamaki, wadannan ’yan wasan sun samu hanyar dawowa domin buga wa jihohinsu wasa, wanda hakan ya haifar da tabarbarewar gasar,” inji shi.
Wakilinmu ya tattaro cewa, wani babban jami’in hukumar wasanni makarantu ya kare ’yan wasan da suka fito daga jiharsa, wadanda aka gano sun haura shekaru amma suka samu damar buga wasan.
Majiyarmu ta ce, “Abin bakin ciki ne, babban jami’in hukumar wasanni na makarantar ya goyi bayan duk abin da ke haifar da matsalar baki daya, an gano ’yan wasa daga jihohin sa sun wuce shekaru.
“An tantance su, amma sun yi wasa da abokan karawarsu, yayin da jihar Yobe ta yi nasara a kan Jigawa kuma an gano cewa sunsa ’yan wasa sun wuce shekaru, an gano wasu ’yan wasan da aka dauko su daga makarantun gaba da sakandire.
“Wasu daga cikin ’yan wasan da ba su wuce gona da iri ba tsofaffin daliban makarantun ne, duk da cewa ka’ida ta bayyana cewa wannan gasa ta musamman ce ga daliban da ba su wuce ajin na biyu na babbar sakandire (SS2) ba, an yi amfani da kimar gasar ta hanyar kokarin cin nasara ko ta halin kaka.”
Wata majiya mai tushe ta ce “Na shafe sama da shekaru 15 ina shiga wannan gasar a matsayin daya daga cikin ma’aikatan dakin bayan fage.
Majiyarmu ta yi zargin cewa, “Wannan ita ce gasar Milo mafi muni, wasu ’yan wasan ba su saka kayayyakin tallan gasar ba, kamar yadda yake a aladarta ta yin amfani da cewa daga rana daya ’yan wasan kan samu isashen abin sha na Milo,kayan kyaututtuka, hakan na nuni da cewa lallai akwai inda aka samu matsala.
“Daga ranar litinin har zuwa yau ba a bai wa kowa ko kofi daya ba, hatta ‘yan wasa, ko jami’ai, babu ko da dede da dan kankanin Milo da aka bayar a wurin taron.
“A gaskiya abin da ya fi ban mamaki shi ne rashin abubuwan ban sha’awa na gefe da kuma nishadantarwa wadanda yawanci ke tare da gasar sun ɓace, ina tabbatar da cewa wannan shine mafi munin gasar Milo.”