Rashin lafiyar alkali ya janyo dage ci gaba da zaman shari’ar da ake yi tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da malamin addinin Musuluncin nan na Jihar, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
A ranar Alhamis ce dai aka tsara ci gaba da zaman a Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a birnin Kano, wacce Mai Shari’a Ibrahim Sarki-Yola ke jagoranta.
- NAJERIYA A YAU: Gudunmawar da kowa zai bayar wurin kawar da ta’addanci
- Ana zargin matashi da sace ’yar yayarsa, ya kashe ta sannan ya binne ta a tsaye
Kakakin Kotunan Shari’ar Musulunci na Jihar Kano, Muzammil Ado Fagge shi ne ya shaida wa manema labarai hakan a ofishinsa.
Za a iya cewa wannan shi ne karo na farko da aka samu kotun ba ta zauna ba tun daga lokacin da Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Abduljabbar Kabara a gaban kotun a ranar 16 ga watan Yulin 2021 inda take zargin shi din da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W) da tayar da hankulan jama’a.
A cewar Muzammil Ado Fagge, saboda haka, kotun za ta ci gaba da sauraren shariar a ranar biyu ga watan Yunin 2022.
A zaman da ya gabata, kotun ta dage shari’ar sakamakon rashin lauya ga Abduljabbar Kabara, lamarin da ya janyo alkali ya nemi Hukumar Agazawa Sharia ta Kasa (Legal Aid Council) da ta ba wa malamin lauyan da zai tsaya masa.
Idan dai za a iya tunawa wannan shi ne karo na uku da lauyoyin Abduljabbar Kabara suke ficewa daga shari’ar tasa.