Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Kano ta sanya ranar 29 ga watan Satumban 2022 don kammala tattara bayanai a shari’ar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Malamin dai na fuskantar zargin batanci ne ga Annabi Muhammad (S.A.W) da yunkurin tayar da zaune tsaye a kotun wacce Mai Shari’a Ibrahim Sarki-Yola yake jagoranta.
- Ta sayar da jaririnta N600,000 mako 3 bayan haihuwarsa a Ogun
- Dalibin jami’a ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da tabarya, ya karya mahaifinsa
Bayan dawo wa zamanta ranar Alhamis, kotun ta ba lauyan da yake kare wanda ake tuhuma, Barista Dalhatu Shehu Usman, damar ganawa da wanda yake karewa a gidan gyaran hali.
Sheikh Abduljabbar ne dai ya roki kotun ta ba shi damar bayan ya yi korafin cewa bai sami damar ganawa da shi ba tsawon lokaci.
Tun da farko dai, daya daga cikin lauyoyin Abduljabbar, Barista Ibrahim Salihu Paki, ya roki kotun ta saki tare da wanke wanda yake karewa sannan ta sanya sabuwar rana domin kammala tattara bayanan.
Sai dai lauyan gwamnati, Barista Suraj Sa’ida, ya soki bukatar lauyan wanda ake tuhumar, inda ya nemi kotun ta yi amfani da bayanai da hujjojin da aka gabatar a gabanta.
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Ibrahim Sarki-Yola, ya ba lauyan Abduljabbar damar ziyartarsa a gidan gyaran halin ranar 27 ga watan Agustan 2022, sannan ya ba shi dukkan taimakon da yake bukata.
Ya kuma umarci dukkan bangarorin biyu su mika bayanansu a rubuce, sannan ya dage zaman kotun har zuwa ranar 29 ga watan Satumban 2022 don kammala tattara bayanan.