Wata Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano da ke zamanta a Kofar Kudu ta ki amince wa da bukatar bayar da belin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, malamin nan da ake tuhuma da laifin yin batanci ga fiyayyen halittta, Annabi Muhammad (SAW).
Alkalin kotun Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ne ya bayyana cewa ba za a bayar da belin ba a wannan lokaci yayin da lauyan wanda ake zargi, Barista Ambali Obomeileh Muhd (SAN) ya nemi kotun da ta bayar da belinsa.
Wannan dai na zuwa ne bayan da lauyoyin masu gabatar da kara suka yi suka a bukatar lauyan wanda ake zargi da cewa babu wani kakkarfan dalili da zai sa a bayar da belin nasa.
Wakiliyarmu ta ruwaito cewa kotun dai ta sanya ranar 12 ga watan Mayu 2022 domin yanke hukunci a kan karbar kaset din da ke dauke da karatuttukan wa’azin Abduljabbar Kabara wanda muryar da aka nada a cikinsa ne ake zargin malamin ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Tun da farko ne dai lauyan wanda ake kara, Barista Ambali Obomeileh Muhd (SAN ) ya karanto wa wanda ake zargi kunshin tuhuma ta hudu wadda ake zarginsa da danganta kalmar kwartanci ga Annabi Muhammad (SAW) wanda ya ce hakan yana kunshe a cikin Hadisin Hajah da ke cikin Littafin Bukhari da kuma Muslim.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta wannan tuhumar inda ya bayyana cewa, masu gabatar da kara sun cakuda maganganun da ke cikin karatunsa don a dora masa laifi, yana mai dagewa kan cewa shi kore kalmomin yake yi daga janibin Annabi Muhammad (SAW)
A kan haka ne lauyan wanda ake zargi ya gabatar wa kotun kaset din karatuttukan Abduljabbar Kabara din domin kotun ta saurara sannan ya zama hujja abar nuni ga kotun.
Sai dai Lauyan masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Saida Suraj, ya yi suka game da hakan inda ya ce satifiket din da aka gabatar wa kotun ba na kaset din ba ne don haka akwai shakku a kansa.