Wasu fusatattun matasa a yankin Gangare dake kusa da Kasuwar Mile 12 a Karamar Hukumar Kosofe ta jihar Legas sun kai hari kan wani kwamandan kato-da-gora na yankin bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).
An dai kai wa mutumin mai suna Haladu Muhammad harin ne ranar Juma’a, kuma ko kafin jami’an tsaro su zo gurin tuni har an banka wa motarsa wuta tare da lalata ofishinsa.
Wani ganau a inda lamarin ya faru, Usman Adamu Sarauta ya shaidawa Aminiya cewa matasan sun kuma kai hari kan jami’an tsaron da suka zo wurin bayan an yi musu kiran gaggawa.
Ya ce, “Suna zarginsa ne da yin batanci ga Annabi (S.A.W), ko da yake ba za a iya tabbatar da gaskiyar hakan ba. Allah ne masani.
“A kan ido na aka kona motarsa sannan suka lalata ofishinsa. A unguwar nake zaune, kuma na san yadda mutane suke korafi a kan yadda yake gallaza musu. Watakila wannan dalilin ne ya sa suka yanke shawarar huce takaicinsu ta wannan hanyar,” inji Usman Sarauta.
Kazalika, wani mazaunin unguwar shima ya ce kiris ya rage matasan su ritsa da Haladun yayin harin, amma ya samu ya gudu sai wasu yaransa da abin ya shafa.
“Allah ya taimake shi ya sha da kyar bayan jami’an tsaro sun kubutar da shi, amma an kai harin kan wasu daga ciki yaransa. Mutane ma na cewa har an kashe wasu daga cikinsu, amma babu tabbaci kan haka.
Gungun matasan sun zo ne suka rika jefa duwatsu a kan jami’an tsaro, na kuma ji ana cewa wani harsashi ya sami wata mata har ta mutu nan take,” inji majiyar.
Wakilin Aminiya ya rawaito cewa yanzu haka an girke jami’an tsaro a unguwar don kwantar da tarzoma.