✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin almundahana: Sakataran Karamar Hukumar Zariya ya ajiye aiki

Sakataran Karamar Hukumar Zariya Dokta Aminu Kwasau ya ajiye aikinsa tare da mika dukkan kayayyakin karamar hukumar da ke hannunsa. Majiyar Aminiya ta ce a…

Sakataran Karamar Hukumar Zariya Dokta Aminu Kwasau ya ajiye aikinsa tare da mika dukkan kayayyakin karamar hukumar da ke hannunsa.

Majiyar Aminiya ta ce a ranar Litinin da ta gabata ce sakataran Dokta Aminu Kwasau ya ajiye aikin bisa wasu dalilai na kashin kansa.

Da Aminiya ta tuntube shi ta waya, Dokta Aminu Kwasau ya ce a daidai wannan lokacin yana Maiduguri a jihar Borno inda yake halartar taron bita da zai kwashe mako biyu amma in ya dawo zai yi bayani.

Ajiye aikin da sakataran ya yi ya zo ne daidai da lokacin da Hukumar EFCC da ICPC da kuma kwamitin bincike da ma’aikatan kula da kananan hukumomi ta jihar Kaduna ke kai komo a kai a Karamar Hukumar Zariya.

Wata majiya mai karfi ta tatabbatar da ajiye aikin sakataran, inda majiyar ta ce tabbas sakataren ya ajiye aikinsa ne saboda yanayin yadda ya ga al’amura na  gudana a karamar hukumar na rashin tsafta, don haka ya ce gara ya koma aikinsa na koyarwa ya fi mishi alheri.

Shi ma da aka tuntube shi ta waya, Shugaban Karamar Hukumar Zariya Injiniya Aliyu Idris Ibrahim ya ce bai da masaniyar ajiye aikin da sakataran Karamar Hukumar ya yi ba.

Sai dai kuma Shugaban Karamar Hukumar ya ce zai umurci daya daga cikin hadimansa da a shirya yadda za a zauna domin ya yi bayanin halin da ake ciki, da kuma irin yadda Karamar Hukumar Zariya ke gudanar da harkokinta, amma har zuwa lokacin hada wanna labarin ba wanda ya kira don karin bayani.