A makon da ya gabata ne fitaccen matashin dan kwallon kafa, dan kasar Spain Thiago Alcantara ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa.
Lamarin dai ya zo wa magoya bayansa da ba-zata ganin ana kallon har yanzu matashin, wanda yake Kungiyar Liverpool ta Ingila yana kan ganiyarsa.
Wannan ya sa Aminiya ta zakulo wasu daga cikin zaratan ’yan wasa da rauni ya tilasta musu yin ritaya alhali da sauransu.
Jack Wilshere
A ranar 8 ga Yulin 2022 ce, Wilshere ya yi ritaya daga kwallon kafa yana da shekara 30 a duniya.
Matashin dan kwallon ya fara buga wa Arsenal ne yana dan shekara 16 a duniya, amma a lokacin da ya cika, ya fara tumbatsa, sai rauni ya hana shi sakat, tun bayan karyewa da ya yi a shekarar 2011.
Shi kansa Wilshere ya taba bayyana cewa, “Ban kai matakin da ya kamata in kai ba a kwallon kafa. Abu ne marar dadi, amma babu yadda zan yi.”
Mario Gotze
A wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya na 2014, Gotze ya zura kwallon da Jamus ta doke Ajantina da ci daya mai ban haushi, inda bayan wasan aka fara kwatanta shi da Messi.
Wasu ma suke cewa ya fi Messi basirar taka leda a lokacin yana da shekara 22.
Amma rauni ya hana dan wasan cika abubuwan da aka yi zato a game da shi, inda yanzu haka yake ci gaba da lallabawa a Kungiyar Eintracht Frankfurt.
Paul Pogba
Paul Pogba wani dan wasa ne da babu wanda ke kokwanton kwarewarsa wajen taka leda, ba don yawan samun rauni ba.
Bayan ya sha fama da rauni a Manchester United, dan wasan ya koma Juventus, inda ya fara wasa a ranar 14 ga Mayun 2023, bayan dadewa bai buga wasa ba kasancewar ya dawo kungiyar da rauni.
Amma minti 23 da shiga wasan, ya sake samun wani rauni, inda nan take ya fashe da kuka.
Yana cikin wannan jinyar ce kuma aka kama shi da laifin amfani da maganin kara kuzari, inda aka yanke masa hukuncin nisantar harkokin kwallon kafa na shekara hudu.
Thiago Alcantara
Lokacin da Guardiola ya koma Kungiyar Bayern Munich, ya bayyana wa hukumar kungiyar cewa dole a sayo masa Thiago Alcantara, ko ya fasa aiki da su.
Matashin dan wasan wanda yake da jinin Brazil da Spain dan wasan tsakiya ne da ya kware wajen takawa da raba kwallo.
Bayan dawowarsa Liverpool, an yi tunanin ya warke, amma haka ya ci gaba da jinya, amma duk wasan da ya buga yakan nuna bambanci.
Tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya bayyana a lokacin cewa, “Ina so in yaba wa Thiago, amma ina tsoron da zarar na yaba masa, sai kwatsam ya ji rauni!”
Sauran wadanda raunuka dabandaban suka hana rawar gaban hantsi sun hada Marco Reus, wanda duk da ya ci gaba da taka leda, amma ba a matsayin da aka yi hasashe ba a lokacin da ya fara.
Da Michael Owen, wanda ya lashe Kambin Ballon d’Or yana dan shekara 21, inda aka yi tsammanin zai lashe kambin Ballon d’Or sau da dama, amma raunin ya hana shi cim ma nasarar haka.
Wani matashin dan wasan da dole rauni ya tilasta shi yin ritaya shi ne Eden Hazard, wanda tun zuwa Real Madrid yake fama da rauni, wanda hakan ya sa aka samu kwan-gaba-kwan-baya a tashensa a kulob din.
Ana tsaka da sauraron ya dawo ganiyarsa ce matashin dan wasan ya sanar da yin ritaya daga tamaula, inda ya bayyana cewa ya gaji haka.
Haka shi ma Ronaldo Delima, wato Ronaldo na Brazil, rauni ne ya hana shi rawar gaban hantsi, inda duk da kasancewarsa dan wasan gaba da ake tunanin babu kamarsa a lokacin da yake tashe, dole ya yanke shawarar yin ritaya domin jikin ya huta.
Akwai kuma wasu irin su Marco van Basten da Adriano da Luis Saha da Youan Gourcuff da sauransu.