✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar tsadar rayuwa ta ci rai a Albaniya

An yi dauki-ba-dadi tsakanin ’yan -sanda da masu zanga-zanga a ofishin Fira Minsitan Albaniya

Mutum daya ya rasu, wani kuma na hannun ’yan sanda bayan dauki-ba-dadi tsakanin ’yan sanda da masu zanga-zanga a kasar Albaniya.

An yi artabun tsakanin ’yan sanda da masu zanga-zangar ne a kofar Ofishin Fira Mistan kasar, Edi Rama, bayan masu zanga-zangar sun yi kokarin yin kutse.

Dubban ’yan kasar ne suka fito kan titi domin zanga-zangar kan tsadar rayuwa da kuma rashawa da ta yi wa kasar tasu katutu.

Sai dai wasunsu sun keta sahun ’yan sandan da karfin tuwo zuwa kofar Fira Ministan, inda suka rika yin zane-zanen bakin fenti da kuma ja.

’Yan sandan sun kama mutum daya a cikin masu zanga-zangar, yayin da wani mutum guda ya rasu a ofishinsu.

Da farko an yi zanga-zangar cikin lumana na kusan awa uku, daga bisani suka watse.

Kasar Albaniya na fama da hauhawan farashin kayan masarufi, inda aka ninka farashin abinci da mai da sauran kayan bukatu.

Hakan ya faru ne sakamakon mamaye kasar Ukraine da Rasha ta yi.

Al Jazeera