✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar Kungiyar Kwadago ba za ta shafi sufurin jirage ba —NUATE

Kungiyar Ma’aikatan Jirgin Sama ta Najeriya (NUATE) ta ce zanga-zangar lumanar kungiyar Kwadago ba za ta shafi tashin jiragen sama ba a kasar. Babban Sakataren…

Kungiyar Ma’aikatan Jirgin Sama ta Najeriya (NUATE) ta ce zanga-zangar lumanar kungiyar Kwadago ba za ta shafi tashin jiragen sama ba a kasar.

Babban Sakataren kungiyar, Kwamaret Ocheme Aba ne ya bayyana wa Aminiya hakan inda ya ce wannan kuma ba zai shafi shiga zanga-zangar da kungiyar za ta yi ba.

A ba ya ce kungiyar ta amsa kiran kungiyar kwadago na fita zanga-zangar bai-daya a ranakun Talata da Laraba, don nuna kin amincewarsu da yadda da gwamnati ta ki kawo karshen yajin aikin ASUU, SSANU, da NASU.

Babban Sakataren ya kuma ce wannan somin tabi ne kan matakin da Kungiyar ta NUATE za ta dauka, matukar gwamnatin ta gaza kawo karshen yajin aikin.

“Don haka ma’aikatanmu su zama cikin shirin samun sanarwarmu ta gaba, idan ta kama mu tsunduma yajin aiki za mu yi, kuma hakan na iya zuwa nan da kowanne lokaci”, in ji shi

Sai dai ya ce zanga-zangar ba a kusa da filayen jirgi za a gudanar da ita ba, a karkashin gadar Ikeja ne zuwa Alausa a yi a Legas.