Wani masanin harkar tattalin arziki, Dakta Aminu Usman ya ce akwai yuwuwar hauhawar farashin kayayyaki ya kara ta’azzara muddin sace-sacen da zauna-gari-banza ke yi da sunan zanga-zangar #EndSARS ya ci gaba da tilastawa shaguna da kamfanoni rufewa musamman a jihar Legas.
Dakta Aminu wanda shine shugaban tsangayar Nazarin Halayyar Dan Adam ta Jami’ar Jihar Kaduna ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarun Najeriya a Abuja ranar Litinin.
Ya ce takaita zirga-zirga a Legas zai shafi safarar kaya zuwa jihar da rarraba kayan abinci daga can zuwa wasu jihohin na kudancin Najeriya.
Masanin ya ce abinda zai biyo bayan zanga-zangar ba zai haifar wa da kasar da mai ido ba musamman kasancewar ba ta dade da murmurewa daga kullen annobar COVID-19 ba.
A cewarsa, “A takaice, akwai yuwuwar Najeriya ta sake fadawa masassarar tattalin arziki a karo na biyu cikin shekaru hudu bayan farfadowarta daga ciki a 2016.
“Legas ita ce cibiyar cinikayyar Najeriya, kuma tsaiko na rana daya zai yi mummunar illa ga kasar baki daya, ballantana kuma ka yi maganar girman barnar lalata dukiyoyin gwamnati da na mutane masu zaman kansu,” inji shi.
Ya ce babu wani mai sha’awar zuba jari da zai yi marmarin narka dukiyarsa a kasa ko jihar da mutanenta ke daukar doka a hannunsu gwamnatinta kuma ta zauna ta nade hannuwanta tana kallo.
“Yawan kudin da ake bukata domin sake gina wuraren da aka lalata kamar yadda gwamnatin jihra Legas ta yi kiyasi na nufin lalitar gwamnati za ta koka sosai kenan kafin abubuwa su sake daidaita.
“Ka ga kenan hatta kasafin kudin 2021 na gwamnatin Legas da na Gwamnatin Tarayya ba lallai ne a aiwatar da shi yadda ya kamata ba.
“Shirye-shiryen da aka yi domin wasu muhimman ayyuka yanzu dole a karkatar da kudadensu kenan wajen gyara barnar da aka yi,’’ inji Dakta Usman.
Masanin ya kuma ce matsalar ba wai iya jihar Legas za ta shafa ba, har ma da sauran jihohi.
Mutane da dama ne suka rasa ransu, dukiyoyin biliyoyin Nairori kuma suka salwanta ko dai sanadiyyar konawa, lalatawa ko sacewa a sassa da dama na Najeriya.
A ranar 22 ga watan Oktoba, gwamnan jihar Legas Bababjide Sanwo-Olu ya ce jiharsa ta tafka gagarumar asara sakamakon zanga-zangar da ta rikide ta koma tarzoma a jihar.