Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci kwamitin da zai binciki tarzomar da aka yi lokacin zanga-zangar matsin rayuwa a jihar, da kada su sassautawa duk wanda aka samu da laifi.
Gwamnan, ya bayar da wannan umarni ne, bayan ya ƙaddamar da kwamitin da zai binciki kisan kai, lalata dukiyoyin gwamnati da na mutane, da kuma satar kayayyaki da aka yi yayin zanga-zangar.
- Kifar da gwamnati: ’Yan sanda sun sa kyautar N20m kan bature da ɗan Najeriya
- Ƙasurgumin ɗan daban da ya addabi Kano ya mutu
An fara zanga-zangar lumana ne, wadda daga baya ta rikiɗe zuwa tarzoma a jihar, lamarin da ya haifar da rasa rayuka da kuma asarar dukiya mai tarin yawa.
Gwamna Yusuf, ya bayyana cewa, “Muna da ƙwarin gwiwar yin abin da ya dace ba tare da la’akari da sakamakonsa ba. Ina kira a gare ku da ku yi wannan aiki cikin gaskiya da riƙon amana, domin ciyar da jiharmu da ƙasarmu baki ɗaya.”
Har ila yau, gwamnan ya yi kira ga shugabannin addini da na gargajiya da su taimaka wajen wanzar da ɗabi’un kirki a zukatan matasa.
Gwamnan ya bayyana cewa an kama matasa da dama an kuma gurfanar da su a kotu yayin tarzomar.
Sai dai ya yi kira ga kwamitin da su binciki dalilin da ya sa matasan suka aikata irin waɗannan laifuka a yayin zanga-zangar.
Gwamna Yusuf, ya kuma yi kira ga kwamitin da su tabbatar da cewa ba a yi wa duk wanda aka samu da laifi sadsauci ba.
Kwamitin na mutum 14, wanda tsohon Alƙalin Alƙalai Lawan Wada Mahmoud ke jagoranta, ya yi alƙawarin gudanar da bincike mai zurfi da kuma hukunta waɗanda suka aikata laifukan.