Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ɗage taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), inda ya gana da shugabannin tsaro a Aso Rock.
Ministocin da suka isa wajen taron an hange su suna barin a Fadar Shugaban Ƙasa kimanin ƙarfe 12 na rana.
- An kama tela da wasu 30 kan zanga-zanga da tutocin Rasha a Kano
- An Gano Gurnetin ’Yan ta’adda 6 A Maiduguri
Kaɗan daga cikin ministoci ne suka isa lokacin da aka ɗage taron.
Aminiya ta samu labarin cewa ɗage taron ba zai rasa nasaba da wani taro kan sha’anin tsaro da Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta a fadar shugaban ƙasa.
Ko da yake ba a bayyana ajandar taron ba, ana tsammanin majalisar za ta tattauna kan zanga-zangar da ake yi a yanzu da kuma yanke shawarar matakin da ya dace a ɗauka.
Taron ya biyo bayan jawabin da Shugaba Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya da safiyar ranar Lahadi, inda ya buƙaci masu zanga-zanga su buɗe tattaunawa domin nemo mafita.