✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zanga ta barke a Amurka bayan dan sanda ya hallaka bakar fata

Kisan dai a birnin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shari’a kan masu hannu a kan kisan George Floyd.

Zanga-zanga ta barke a birnin Minneapolis na Amurka bayan wani dan sanda ya harbe wani matashi bakar fata wanda ya mutu a kusa da wurin da aka hallaka George Floyd a bara.

Daruruwan matasa ne dai suka yi cincirindo tare da tunkarar ’yan sanda, sa’o’i kadan bayan an harbe matashin mai suna Daunte Wright a cikin motarsa a birnin na Minneapolis.

Jami’an ’yan sanda a yankin dai sun kashe fitilu tare da harba barkokon tsohuwa a kan masu zanga-zangar da suka taru a wajen ofishin ’yan sandan da suka ja daga saboda shirin ko-ta-kwana.

Kisan dai a birnin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shari’a kan mutum hudu na farko da suke da hannu a kan kisan George Floyd, lamarin da ya janyo zazzafar zanga-zanga a wancan lokacin.

Mahaifiyar Daunte, Katie Wright tun da farko dai ta shaidawa masu zanga-zangar cewa dan nata ya kirata kafin mutuwarsa yana shaida mata cewa ’yan sanda sun tsare shi.

Ta ce a lokacin ta jiyo yadda suke umartarshi da ya kashe wayar, kafin wani daga cikinsu ya kasheta ta karfin tsiya.

Jim kadan ne kuma budurwar dan nata ta sanar da ita cewa sun harbe shi.

Ta ce, “Kawai abinda ya yi shine yana amfani da sinadarin sa kamshi a motarsa, sai suka umarce shi da ya fito daga ciki.

“Fitowarsa ke da wuya sai budurwarsa ta ce suka harbe shi. Nan take ya koma cikin motar da nufin tsira da rayuwarshi sai ya fadi, yanzu kuma ya mutu. Babu wanda ya ce mana uffan a kai,” inji mahaifiyar.

Sai dai ’yan sanda a birnin cikin wata sanarwa sun ce jami’ansu sun fito da wani direba ne ranar Lahadi bisa zargin karya dokokin tuki, ko da suka ga dama akwai wani laifin da ake tuhumarsa da shi sai suka yi kokarin tafiya da shi.

Hakan ne a cewarsu ya sa ya yi kokarin komawa cikin motarsa, lamarin da ya sa wani dan sanda ya yi harbi a kuskure harsashi kuma ya same shi.

’Yan sandan sun kuma ce motar marigayin sai da ta yi tafiya mai nisa kafin ta je ta tunkuyi wata motar sannan matashin ya mutu nan take..

Wata mata dake zaune a kusa da inda lamarin ya faru, Carolyn Hanson ta ce ta ga lokacin da jami’an tsaro suke kokarin jawo mutumin daga cikin motarsa jina-jina.