✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zanga-zanga kan sanya Hijabi: Iran ta dakatar da ayyukan ’yan Hisbah a kasar

Kasar Iran ta dakatar da ayyukan dakarun Hisbah a kasar a cewar rahotanni da ke fitowa daga kafofin yada labarai na cikin kasar.   Labarin…

Kasar Iran ta dakatar da ayyukan dakarun Hisbah a kasar a cewar rahotanni da ke fitowa daga kafofin yada labarai na cikin kasar.  

Labarin dakatarwar ya fito ne daga bakin babban mai gabatar da kara na kasar, Mohammed Jafar Montazeri, a yayin da ya ke gabatar da wani jawabi a wani taro a Teheran a safiyar Asabar.

Gidan talabijin na Al-Jazeera ta rawaito Montezeri na cewa, tsarin aikin Hisbah ya kusa zuwa karshe a kasar, sakamakon yadda zanga-zangar hijabi ta ki karewa a kasar, ke da nasaba da sa hannu kasashen waje.

“Aikin ‘yan Hisabah ba su da alaka da ayyukan Ma’aikatar Shari’a ta kasar, kuma an rufe ta, kamar yadda aka kaddamar da ita daga wannan tushe a baya.” In ji Montazeri yayin amsa tambaya kan dakatar da Hisbah a taron.

Baya ga wannan furucin, babu wasu bayanai da ke tabbatar da dakatar da aikin ‘yan Hisban da ke sintiri a kan titunan kasar lungu da sako su na hana ‘badala’.

Sai dai babban jami’in gwamnatin mai mukamin kwatankwacin na Ministan Shari’a a Najeriya, bai fito fili ya ce an soke Hisbah baki dayanta ba.

Kasar Iran na fama da zanga-zanga ne tun bayan da wata mai suna Mahsa Amini ta mutu a hannun ‘yan Hisbah bayan da suka kama ta bisa laifin kin sanya hijabi, wanda hakan ya fusata jama’a.