Wasu masu zanga-zanga sun kone gidan tsohon Shugaban Addini na Iran, Ayatollah Khomeini.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da daddare a inda rahotanni da kuma hotunan bidiyo suka karade shafukan intanet na gidan na ci da wuta.
- Iran na da take-taken kai mana hari – Saudiyya
- Rashin lafiya ne ya kashe Mahsa Amini, ba ’yan Hisbah ba —Iran
Kamfanonin dillancin labarai sun tabbatar da sahihancin bidiyon, da kuma inda aka dauke su, da ke nuna cewa gidan shugaban ne ke ci da wuta, ana kuma jin muryoyi na shewa da tafi cikin murna.
Gidan wanda a nan ne aka haifi Jagorar juyin-juya-hali, wanda kuma aka mayar da shi gidan adana tarihi domin girmamawa ga tsohon shugaban mai farin jini.
Kona gidan da aka haifi Ayatollah na daga cikin ayyukan kin jinin gwamnati na baya-baya nan da masu zanga-zanga ke ci gaba da yi a kasar domin kalubalantar Ayatollah Ali Khamenei da kuma gwamnatinsa.
A cikin jerin zanga-zangar da a ke ta yi a kasar tun bayan mutuwar Mahsa Amini wata ‘yar shekara a 22, yayin da ta ke tsare a hannun ‘yan Hisbah a bisa laifin rashin sanya hijabi a watan Satumba.
Ofishin hulda da ‘yan jaridun na Khomein ya musanta kona ofishin a wani sakon sa ga kamfanin dillancin labarai na Taslim.
Imam Khomein shi ne shugaban juyin-juya hali na farko bayan da ya samu nasarar tuntsurar da mulkin sarki Shah Reza Phlavi a shekarar 1979 mai ra’ayinn turawan yamma, ya rasu ne a shekarar 1989 bayan rashin lafiya.