Jam’iyyar APC ta bayyana cewa rashin sanin makamar aiki ya sanya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yake ɗora wa ’yan adawa alhakin gazawarsa.
Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan a matsayin martani kan zargin da gwamnan ya yi na ɗora wa jam’iyyar alhakin yadda zanga-zangar tsadar rayuwa ta rikiɗe zuwa tarzoma a jihar.
- An naɗa sabbin shugabannin Ƙungiyar Kano Pillars
- Yadda ma’aikaci zai kashe mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70 a Nijeriya
Ana iya tunawa cewa, Aminiya ta ruwaito Gwamna Abba Kabir Yusuf yana zargin wasu ’yan jam’iyyar APC na jihar da fakewa a cikin masu zanga-zangar suka riƙa fasawa da sace kayan gwamnati da na al’ummar jihar.
Sai dai da yake martani, Abbas ya ce “Duk abin da ya faru sai ya [Gwamnan Kano] ce mu ne.
“Na fahimci kamar har yanzu ya kasa gane cewa shi [gwamnan] yanzu mai mulki ne ba dan adawa ba, duk wata gazawarsa a matsayinsa na gwamna sai ya ce ’yan adawa ne”.
Shugaban jam’iyyar na APC ya ce ba wani dan jam’iyyar APC da yake da ruwa a abubuwan da suka faru a jihar.
Ya bayyana cewa duk wadannan abubuwa da ke faruwa a jihar gwamnan ne ya kirawo ruwa kuma ruwan ya kare a kansa.
“Kowa ya san yadda malamai su kai ta gaya wa al’umma illar yin zanga-zanga har ma suka ce haramun ce a Addinin Musulunci.
“Amma ranar Laraba kowa ya ji gwamnan da kansa shi ya ce a fito a yi zanga-zangar kuma shi zai fito ya karbe su, to shi ne suma matasan suka ga tunda an gayyace su bari su je su ci irin ganimar da yake ci a gidan gwamnati,” inji Abbas
Ya kara da cewa suna da labarin yadda wasu jami’an Gwamnatin Kano suka yi taro da mafarauta kusan rukunonin 70, “ka je ka bincika ko ka sa ’yan sanda su bincika maka, in kuma ba ka da labari to mu mun san lokacin da aka yi da wurin da aka yi da kuma wadanda suka yi.”
Abdullahi Abbas ya kuma shawarci gwamnan da ya mai da hankali wajen yi wa al’ummar jihar Kano aiki kafin lokaci ya kure masa, maimakon ɗora alhakin gazawarsa kan ’yan adawa.