An sa dokar hana zirga-zirga ta awa 24 a Kano bayan zanga-zangar tsadar rayuwa ta rikide zuwa tarzoma a jihar.
Hakan na zuwa ne bayan ’yan sanda sun kuma kama mutane 269 kan fasa shaguna da sace kayan ciki a lokacin zanga-zangar.
Daga cikin mutanen da aka kama har da matasan da suka dauki makami tare da tayar da rikici a yayin zanga-zangar a rana Alhamis.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Kano, wanda ya gabatar da wadanda ake zargin ya bayyana cewa sun raunata jama’a tare da lalata dukiyoyin jama’a da kayan gwamnati a yayin zanga-zangar da ta rikide zuwa bore.
- NAJERIYA A YAU: Kuskuren Da Gwamnati Ta Yi Har Aka Fara Zanga-Zanga
- Masu zanga-zanga sun kai ziyara gidan Buhari a Daura
- An sanya dokar hana fita a ƙananan hukumomi 3 a Yobe
Jami’in ya kuma nuna kayan da aka kwato a hannunsu da suka hada da kayan abinci da sauransu da suka kwashe a wuraren da suka fasa.
A cewarsa, wadanda ake zargin za su ci gaba da kasancewa a tsare zuwa lokacin da shashen binciken laifuka na rundunar zai kammala bincike domin garfanar da su a gaban shari’a.
An kama 25 a Jihar Nasarawa
A Jihar Nasarawa kuwa, mutane 25 ne aka kama bisa zargin fasa shaguna da kwashe kayan jama’a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa a garin Keffi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Umar Shehu-Nadada, ya shaida wa wakilinmu cewa an shawo kan masu zanga-zangar..
A cewarsa, bata-gari da kananan yara na daga cikin wadanda suka shiga zanga-zangar suka haddasa rikici.
A jihar dai, an sanya dokar hana fita a yankin Mararaba da wasu garuruwa da ke Karamar Hukumar Karu sakamakon tashin rikici.
Shugaban Karamar Hukumar, James Thomas, ya sanar da haramta zirga-zirga daga karfe 6 na yamma zuwa 6 ba safe a wuraren.”