✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kafa a dokar hana fita a Jigawa

Za a sassauta dokar daga karfe 12 zuwa 2 na rana domin ba wa jama'a damar halartar Sallar Juma'a.

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanya dokar hana fita ta tsawon Sa’a 24 kan rikincin da ya biyo bayan zanga-zangar tsadar rayuwa.

Gwamna Umar Namadi be ya sanar da dokar tare da umartar jami’an tsaro su dauki mataki masu masu kunnen kashi.

Sai dai ya ce za a sassauta dokar daga karfe 12 zuwa 2 na rana domin ba wa jama’a damar halartar Sallar Juma’a.

“Ba za mu lamunci yadda aka juyar da zanga-zangar lumana zuwa tashin hakali da sace-sace ba, don haka dole mu taka mata burki.

 

“Domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mun kafa dokar hana fita ta tsawon sa’a 24.

“Amma kasancewar yau Juma’a za a sassauta dokar daga karfe 12 zuwa 2.30 ma rana domin a samu gabatar da Sallar Juma’a

“Gwamnatin da hukumomin tsaro za su ci gaba da lura da halin da ake ciki domin tabbatar da tsaron dukiyoyi da rayukan al’ummar jihar,” in sanarwar da gwamnan ya gabatar a kafofin watsa labarai a safiyar Juma’a.