✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zanen batanci ya kara tsamin dangantaka tsakanin Iran da Faransa

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi sammacin shugaban ofishin jakadancin Faransa a kasar bisa tsamin dangantaka

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta shugaban ofishin jakadancin Faransa a kasar bisa tsamin dangantakar da ya biyo bayan zanen batanci ga manzon Allah (S.A.W) da kasar ta yi.

A makon nan ne Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ’yan kasarsa na da ’yancin wallafa kowane irin zanen batanci, kalamin da ya jawo la’anta daga kasashen Musulmai da dama.

Kamfanin Dillancin Labaran Kasar Iran (ISNA) ya rawaito cewa, “Muna Allah-wadai ga kowanne irin batanci ga Ma’aiki da kuma irin matsayar da hukumomin Faransa suka dauka a kan hakan.”

Ma’aikatar ta yi takaicin kan yadda aka keta alfarmar miliyoyin Musulmai da sunan ’yancin fadin albarkacin baki a Faransa.

Iran ta kuma yi gargadin cewa lamarin zai kara rura wutar gaba tsakanin Faransa da sauran Musulmai.

Kafafen watsa labaran kasar sun nuna an shirya gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Faransa a Iran.

Idan dai za a iya tunawa a ’yan watannin baya ne Jaridar Charlie Hebdo ta sake wallafa zanen batanci ga Ma’aiki.

Zanen batancin dai ya janyo Allah-wadai daga al’ummar Musulmin duniya inda har wasu ke kiran a kaurace wa amfani da kayan da aka sarrafa a Faransa a domin ladabtarwa.