Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ba shi da burin tsayawa takarar shugabancin Najeriya sai dai idan Shugaba Muhammadu Buhari ne ya umarce shi da yin hakan.
El-Rufai ya yi wannan jawabin ne a shirin siyasa a yau wato “Politics Today,” na Gidan Talabijin na Channels, yayin da aka nemi jin ta bakinsa kan rade-radin da ake yi na cewa shi da Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi na son tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
- Dalilin da Buhari da gwamnoni 19 suka kori Mai Mala Buni —El-Rufai
- Rikicin Ukraine: Birtaniya ta kwace kadarorin Abramovich
Gwamnan ya ce: “na sha fadin cewa ba ni da burin tsayawa wata takara a zabe mai zuwa, kawai mutane ne suka gaza yarda, amma Amaechi idan yana da ra’ayi yana da damar tsayawa amma ni ba ni da ra’ayi ba na neman wani abu.”
Ko da aka tambayi gwamnan idan kuma Buhari ya nemi ya tsaya takara a matsayin shugaban na wanda ya ke ganin kimarsa da mutunci, El-Rufai ya bayyana cewa zai yi kokarin fahimtar da shugaban kasar dalilan da ya sa ba zai yi takarar shugabancin kasar ba duba da yanayi na shekarunsa da suka ja da kuma gajiya.
“Wannan kuma magana ce ta daban. Zan tattauna da shugaban kasa kuma zan bayyana masa dalilan da ya sa ba ni da ra’ayin tsayawa takarar, amma idan ya dage zan yi,” a cewar gwamnan.