✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan so mu kasance tare da Messi a kulob daya –Ronaldo

Shahararren dan qwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ce yana so su hadu da shahararren dan qwallon FC Barcelona na Sifen Lionel Messi a kulob…

Shahararren dan qwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ce yana so su hadu da shahararren dan qwallon FC Barcelona na Sifen Lionel Messi a kulob daya da hakan zai bashi damar cigaba da lashe kyautar Gwarzon dan qwallon duniya ba tare da matsala ba.

dan qwallon ya yi wannan furuci ne jim kadan bayan ya lashe Gwarzon dan qwallon duniya a karo na 4 a ranar Litinin da ta wuce.
Ya ce “zan so in yi wasa tare da Lionel Messi a kulob daya, don shi ma dan wasa ne da ake ji da shi a duniya, kuma hakan zai cigaba da ba ni damar lashe kyaututtuka masu yawa.”
Da aka tambaye shi ko zai iya lashe kyautar Gwarzon dan qwallon duniya fiye da hudu da suna tare da Messi, sai ya ce ba zai iya amsa wannan tambaya ba. Kowa yana mutunta Lionel Messi ganin yadda ya lashe kyautar Gwarzon dan qwallon duniya sau biyar, inji Ronaldo.
Messi ne ya kafa tarihin dan qwallon da ya lashe kyautar Gwarzon dan qwallon duniya sau biyar. Ronaldo ne ke biye da shi bayan ya lashe sau hudu.