✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan magance rikicin Filato idan na zama Shugaban Kasa – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin magance rikice-rikicen da ake fama da su…

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin magance rikice-rikicen da ake fama da su a Jihar Filato idan ya zama Shugaban Kasa.

Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin ne, lokacin da yake jawabi a filin Folo na Jos, lokacin kaddamar da yakin neman zabensa a garin Jos, a ranar Asabar da ta gabata. Ya ce “Na farko na daukar muku alkawarin zan dawo da zaman lafiya a Jihar Filato. Kuma na yi alkawari zan samar wa matasa ayyukan yi.”

Ya ce gwamnatin APC ta gaza, don haka ba ta iya magana da al’ummar Najeriya, domin ta san al’ummar Najeriya ba za su zabe ta ba. Don haka suke son su yi murdiya a zababbukan da za a yi.

Atiku Abubakar ya ce babu abin da APC ta kawo ga Najeriya, sai yunwa da talauci da rashin zaman lafiya.

A jawabin Daraktan Yakin Zaben Atiku Abubakar kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bakola Saraki ya ce lokacin da Jam’iyyar APC ta karbi mulkin kasar nan, ta yi alkawarin samar da tsaro da samar wa matasa ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki, amma duk ta gaza cika wadannan alkawura da ta dauka.

Ya ce “An wayi gari yau a Najeriya babu tsaro babu abinci sai yunwa. Kuma babu shakka idan al’ummar Najeriya suka zabi Atiku Abubakar zai magance wadannan matsaloli baki daya.”

A jawabin, tsohon Gwamnan Jihar Filato, Sanata Jonah Jang ya ce irin taruwar da al’ummar Filato suka yi a wannan wuri, ya nuna cewa PDP ta cinye zabubbukan da za a yi nan ba da dadewa ba.

“Sun ce ba mu iya ba, amma an ba su sun kasa yi.  Jama’a sun ga irin ayyukan da PDP ta yi a Jihar Filato da Najeriya baki daya. Tunda APC suka karbi mulki babu wani abu da suka yi, sai kawo yunwa da talauci. Don haka a dawo da Atiku Abubakar a zabe mai zuwa, domin shi ne zai magance yunwar da wannan gwamnati ta kawo a Najeriya,” inji shi.