Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi barazanar kawo hargitsi a babban zaben kasa na shekarar 2023 a yankin Kudu maso Yammacin kasar.
Igboho wanda ke fafutikar kare hakkin ’yan kabilar Yarbawa a Najeriya, ya bayyana hakan ne a karshen mako a Osogbo, babban birnin Jihar Osun.
- Dahiru Bauchi ya amince da nadin Sanusi Khalifan Tijjaniyya
- An kama direba da ke tsafi da sassan jikin kananan yara
- An tsinci gawar jariri da aka jefar a juji a Jigawa
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, ikirarin da Igboho ya yi na zuwa ne yayin wani gangami na kabilar Yarbawa, inda mahalartansa suke neman ballewa daga kasar.
Kazalika, yana zargin cewa, Gwamnonin Kudu maso yammacin kasa na sha’awar ballewa amma tsoron hada Gwamnatin Tarayya ta hana su kudin da saba raba wa jihohi duk wata ya hana su furta hakan.
“Babu wata yaudara da za ta sani faduwar gaba, sun ce za a kama ni, kuma babu wanda ya isa ya yi hakan don a yanzu mu ba ’yan Najeriya bane, ba mu da wani hadi da kasar a yanzu, a cewarsa.
“Babu wani zabe da za a gudanar a yankin Yarbawa har sai an bamu kasar ’yan kabilarmu, saboda da farko mahukunta sun yi tunani da wasa muka dauki lamarin yayin da muka nemi ballewa daga Najeriya.
“Duk gwamnoninmu suna tare da mu, daga Oyo, Ogun da Ondo zuwa Ekii, Legas da Osun, duk suna tallafa mana, amma ba za su iya nuna goyon bayansu a sarari ba.
“Kudin da suke samu wata-wata daga Abuja na iya yankewa idan suka fito karara suka bayyana cewa suna tare da mu.
“Saboda haka kar wanda ya sake zaginsu. Gwamna Oyetola ya na da sanin cewa za mu zo Jihar Osun, kuma ya kyale muka shigo. Haka ma dukkan Sarakunan gargajiya suna tare mu,” in ji Igboho.
Kazalika, Mista Igboho ya ce zai yi tawaye da duk wadanda suke adawa da manufarsa.