✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan kafa jam’iyyar da za ta yaki matsalar tsaro — Buba Galadima

Muna da dama mu hada kanmu mu bijiro da wata tafiya.

Fitaccen dan siyasar nan kuma tsohon na hannun damar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Buba Galadima ya yi barazanar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa da ya ce za ta kawo maslaha ga dimbin matsalolin da Najeriya take ciki a yanzu, musamman matsalar tsaro.

Alhaji Buba Galadima ya bayyana haka ne bayan wani taro da Kungiyar Tuntubar Juna ta National Consultative Front ta gudanar a kan halin da kasar nan ke ciki.

Kafar labarai ta BBC, ta ruwaito Buba Galadima yana cewa: “Muna da dama mu hada kanmu mu bijiro da wata tafiya wadda za ta tabbatar da shugabanni na kirki wadanda za su yi aiki don al’umma ba don aljihunsu ba.”

Ya kara da cewa: “Muna da dama da za mu iya tsayar da mutumin da za mu iya rantsar da shi wanda zai yi aiki da kundin tsarin mulkin kasar nan ko kuma mu gyara kundin tsarin mulkin ta hanyar da al’umma suna da bakin da za su fada dole a bi.”

Buba Galadima ya ce baya ga matsalar tsaro, kungiyar siyasar ta kuma tattauna kan matsalolin da suka shafi tattalin arziki tare da gabatar da wasu shawarwari don samar da mafita.

Ya kuma bayyana wasu shawarwari da yake ganin za su kawo gyara a kasar nan kamar bai wa kowane mataki na gwamnati damar tafiyar da mulki ba tare da karan-tsaye ba.

A cewarsa babbar matsalar da ake fuskanta a kasar nan ita ce yadda wadansu matasa suka kasance kara-zube ba tare da samun aikin yi ba, abin da ya ce yana sa wadansunsu daukar makamai “suna tsare hanya suna tare matafiya.