✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan iya fitar da kayar bera zuwa kasashen waje -Aliyu Usman Gwani

Malam Aliyu Usman Gwani tsohon ma’aikacin kamfanin sarrafa tumaturin gwangwani na Dadin-Kowa ne kuma masanin harkar noma. Ya ce idan ya samu tallafi, zai iya…

Malam Aliyu Usman Gwani tsohon ma’aikacin kamfanin sarrafa tumaturin gwangwani na Dadin-Kowa ne kuma masanin harkar noma. Ya ce idan ya samu tallafi, zai iya fitar da kayar bera zuwa kasashen ketare saboda yadda take magunguna. Ya bayyana cewa tun fiye da shekaru 200 Girkawa da Romawa ke amfani da itaciyar wajen yin magunguna. Ya bayyana haka ne kuwa ga wakilinmu, a wata tattaunawa da suka yi a lokacin da ya ziyarci gonarsa a garin Dadin-Kowa yankin karamar Hukumar Yamaltu Deba:

Aminiya: Mene ne kayar bera kuma wane amfani take da shi?
Aliyu Usman: kayar bera wata itaciya ce da a Turance ake kira Aspharagus kuma tana warkar da cututtuka masu yawa, wadanda bincike ya nuna.
Aminiya: Ta yaya aka gano amfanin wannan itaciya kuma yaya ake noma ta?
Aliyu Usman:  Wani Baturen kasar Denmark ne mai suna Fred Christensen ya fara shigo da irin a shekara ta 1992, wanda kamfanin tumaturin suka bukata don fadada ayyukansa. Da ya kawo, sai aka hada ni da shi ya koya min yadda ake noman ta. Aka yafa iri, ya yi wata tara, bayan nan aka dasa shi ya sake yin wata tara, sannan aka fara amfani da shi. Da ma shi sai ya yi wata goma sha shida sannan a fara saransa ana sarrafa shi kuma yakan kai shekara goma ana cin moriyarsa.
Aminiya: Kasancewar Baturen da ya koya maka yadda ake noma shi ya bar aiki a kamfanin daga wancan lokacin ne ka fara noma shi ko sai daga baya?
Aliyu Usman: A lokacin da Baturen ya bar aiki, na yi ta yawo ina fadakar da mutane amfanin Aspharagus, amma ba su amince ba. Har gonakan Baba Mai Mangoro a Yola na je da na Sanata Abdullahi Adamu a Nasarawa,wanda shi ne ma ya karbi shawarin ya ce zai gwada, amma har yanzu bai fara ba. Ganin haka ne ma ya sa yanzu ni na fara noma shi. Banda ni a nan Gombe, ba inda ake noman shi duk kasar nan, sai Jos. Yadda  Allah Ya albarkace mu da kasar noma da muna noma shi da za mu iya fitar da shi kasashen ketare a lokacin da nasu bai yi ba. Na fara noman ne a shekarar 1993 daga nan ne na fara kai danyen itacen Otal din Sheraton da Nicon a Abuja suna sayen kowane kilo a kan Naira dubu daya. Ana cinsa, domin magani ne, amma yanzu ana sayen kowane kilo a kan Naira dubu uku. Idan kana da kadada daya, za ka samu ton uku zuwa hudu, wanda wannan kadada daya  idan aka yi lissafi a kan haka za a iya samun Naira  miliyan tara zuwa goma sha biyu ke nan.
Aminiya: Yanzu kadada nawa kake da shi kuma nawa kake ganin za ka samu?
Aliyu Usman: Yanzu dai a nan garin Dadin-Kowa ina da rabin kadada a garin Baraya kan hanyar Kalshingi, ina da rabin kadada  (Hecta), amma wancan rabin hectan ruwa ya lalata ta, sai dai a wannan rabin hecta, in Allah Ya yarda, zan samu Naira miliyan hudu zuwa shida a shekara daya.
Aminiya: Kamar Naira miliyan hudun da kake hasashen samu ko fin haka, nawa kuma za ka kashe zuwa shekarar?
Aliyu Usman: Zan kashe kamar Naira miliyan daya zuwa da rabi, saboda sai mutum ya sayi firji don ajiyarsa kafin a sarrafa shi da kuma janareta saboda rashin wutar lantarki kuma za ka yi rijista da CAC, saboda kamfanoni da  manyan  shaguna da za a dinga kaiwa a Abuja da wasu sassan jihohin kasar nan.
Aminiya: Shi wannan kayar berar, wadanne irin magunguna yake yi?
Aliyu Usman:  Gaskiya wannan Aspharagus din yana magunguna da yawa. Kafin na san shi din, idan na ji mai maganin gargajiya na cewa ga magani daya, amma yana magunguna da yawa, sai in yi mamaki, amma da na shiga yanar gizo, sai na ga wannan Aspharagus din yana maganin hawan jini da na ciwon koda da na gyambon ciki da ciwon hanta da ciwon typhoid da ciwon mafitsara da al’ada irin na mata da kumburi da habo. Kai ko dutse ne a cikin kodar mutum, idan yana amfani da garin wannan itace, zai warke da sauransu. Idan kuma mutum yana da ciwon da yake damunsa, zai iya shiga yanar gizon ya duba ya ga sauran cututtuka a www.aspharagusfor sai ya sa sunan ciwon.
Aminiya: A ina kuke samun irin wannan itace?
Aliyu Usman: Akan samu irin ne idan an yi oda a kasashen Afirka ta Kudu da kuma Peru ko Italiya.
Aminiya: Ganin cewa wannan itace na magunguna da yawa, wane kira kake da shi ga manoma don ganin sun rungumi nomansa?
Aliyu Usman: Yana da kyau mutane su shigo noman wannan aspharagus din sosai domin ni kadai ba zan iya wadatar da kasar nan da wannan magani ba kuma abun da zan ce kofa ta a bude take wajen taimaka wa duk wanda yake da sha’awar koyon nomansa don mu daukaka sunan Najeriya, wanda ga kudi a wajensa ga kuma magunguna. Sannan mu fara sarrafa shi ana yin kafsonsa da lipton da kuma garinsa, saboda a cikinsa akwai bitamin A, B ,C,D,E da K.
 Aminiya: Wane kalubale ne kake fuskanta wajen noman Aspharagus?
Aliyu Usman: kalubalen shi ne na wutar lantarki wajen busar da danyen itacen, saboda idan za a nika sai ya bushe  don ya zama garin da za a yi amfani da shi kuma ana cinsa ma danye.
Aminiya: Ganin cewa kai masanin noma ne ka taba tuntubar wata jami’a ko kwalejin aikin gona don bai wa dalibansu dama suna nazari a kan wannan itaciya?
Aliyu Usman: Kamar yadda na gaya ma tun farko, ban je kowace jami’a ba, amma dai na je gonar Murtala Nyako don shaida musu alfanun wannan itaciya, amma ba su yi na’am da ita ba, sai dai ina kira ga jama’a da su zo su rungumi noman wannan itaciya don mu farfado da tattalin arzikin kasarmu.