✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan hada kan wanzaman Jihar Kuros Riba- Sarkin Aska

Sabon Sarkin Askan Jihar Kuros Riba Alhaji Usman Baban Aska ya yi alkawarin hada kan wanzaman jihar da kuma ci gaba daga inda mahaifinsa marigayi…

Sabon Sarkin Askan Jihar Kuros Riba Alhaji Usman Baban Aska ya yi alkawarin hada kan wanzaman jihar da kuma ci gaba daga inda mahaifinsa marigayi Alhaji Yunusa Sarkin Aska ya tsaya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya bayan Alhaji Salisu Abba Lawal Sarkin Hausawan Kalaba ya nada shi Sarkin Askan jihar.
 Ya ce: “Za mu jawo sauran abokan sana’a a jiki domin hadin kai da bunkasa wannan sana’a tamu da muka gada iyaye da kakanni, domin mu gudu tare mu tsira  tare.”