✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan biya diyyar mutanen da ’yan bindiga suka kashe a Katsina – Dan takarar Gwamna

Ya ce bai ga dalilin da zai sa gwamnati ta ki biyan diyyar ba

Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin jam’iyyar PRP, Alhaji Imrana Jino ya yi alkawarin biyar diyyar duk mutanen da ’yan bindiga suka kashe a Jihar muddin aka zabe shi.

Ya bayyana hakan ne a wajen taron al’umma da ’yan takarar Gwamnan Jihar, wanda kamfanin Media Trust, mamallaka jaridar Aminiya suka shirya ranar Asabar a Katsina.

Ya ce hakan na daya daga cikin manufofinsa na yaki da ayyukan ’yan bindiga da sauran matsalar tsaron da ta addabi Jihar.

Imrana Jino ya kuma ce bai ga dalilin da zai sa a ce akwai gwamnati a Jiha, amma al’ummarta na cikin hali musamman na biyan diyyar sama da Naira milyan ɗ100 don karbo mutun daya, amma ta gaza biyan diyyar wanda aka kashe bz tare da ya san hawa ba balle sauka.

Ku kasance da shafukanmu a dandalin sada zumunta domin jin yadda take kayawa a wajen taron.

%d bloggers like this: