✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan bayyana sunayen wadanda suka tuntube ni kan zaben Jonathan a 2015 – Farfesa Ango

Farfesa Ango Abdullahi, daya ne daga cikin ’yan Arewa 151 da masu goyon bayan Shugaba Jonathan suke kokarin tuntuba domin mara musu baya a zaben…

Farfesa Ango Abdullahi, daya ne daga cikin ’yan Arewa 151 da masu goyon bayan Shugaba Jonathan suke kokarin tuntuba domin mara musu baya a zaben badi. Farfesan ya tabbatar wa Aminiya cewa har an tuntube shi kan batun da kuma irin yadda suka yi da masu tuntubar, har ya ce nan gaba zai fadi sunayen wadanda suka tuntube shi:

Farfesa Ango AbdullahiAminiya: Yallabai an ce akwai wasu ’yan Arewa da ake son tuntuba su mara wa Shugaba Jonathan baya a zaben badi, ciki har da kai, ko an tuntube ka?
Farfesa Ango: To lallai an turo min mutum biyu, sai dai ba zan fada maka sunansu ba, sun ce sun zo ne domin su roke mu a kan cewa mutuncin da aka san mu da ita da kuma sadaukarwa wai a yi musu. Sai ni, kuma na ce musu a yanzu ne aka san Arewa tana da mutunci har tana da wani abu da take iya sadaukarwa? Wadda a ’yan shekarun baya ban da zage-zage da cin mutunci da wulakanci, ba abin da ake mana, yanzu ne kuma ake ganin muna da wani abu da za mu yi na mutunci da sadaukarwa. Saboda na ce musu in kun zo wurina ne a kan ni kaina, to zan yi muku magana, idan ko kun zo ne a matsayin dattawan Arewa, to ba zan yi muku magana ba, sai dai ku bari sai an kira taro sannan ku zo wurin ku yi bayani. Amma a matsayin ni kadai duk wani hakki nawa ban yafe ba, saboda haka b ani cikin wadanda za su goyi bayan wannan mutum, dama can ban goyi bayansa ba tun daga shekara 2011 kowa ya san haka, to balle a ce kuma har an wuce an kawo yanzu zuwa 2015. Na ce musu a shekarar 2011 ma ban yafe hakkina ba balle yanzu.
Aminiya: To ai cewa aka yi bayan gadon shekara biyu da ya yi shi ya fi cancanta ya kara shekara hudu domin ya hada ya zama ya kara zango daya, kana nufin kai a nan ba ka goyi bayan shi ba?
Farfesa Ango: Ba ni cikin wadanda suka yarda ya kara shekara hudu, a dokar kasa ta aje dole inda marigayi ’Yar’aduwa ya ajiye, shi zai ci gaba har karshen wancan lokaci saboda haka, in shugaba ya rasu koda wata lalura, to mataimakinsa zai ci gaba daga inda aka tsaya har sai ya kai karshen zangonsu. To a kan tsarin Jam’iyyar PDP na sani Kudu za su yi shekara takwas, sannan mu kuma mu shekara takwas, da aka zo namu ya shekara biyu ya rasu dokar kasa tace sauran shekara biyun zango farko mataimakinsa ya karasa. To hankali ya nuna cewa in ya kai, Arewa ta zo ta ci gaba da nata domin ko ba ta samu shekara takwas ba, za ta samu shekara shida, marigayi Umaru ’Yar’aduwa ya yi biyu ga kuma hudu da aka samu, amma wadansu suka tsaya kai-da-fata cewa sai dai a bar shi ya ci gaba, kuma ciki har da ’yan Arewa kuma ’yan Arewa su suka fi yawa.
Aminiya: To ga shi kuma Jonathan bayan ya shekara kusan biyar ba ku dadtawan Arewa ba kusan duk dattawan Najeriya kuna son ku goce masa mae ya kawo haka?
Farfesa Ango: Eh, ni dai na san nawa ban san na saura ba.
Aminiya: Yallabai, na ga daya daga cikin wadanda suka kawo shi ya rubuta masa dogowar wasika yana zarginsa da kasawa, me zaka ce?
Farfesa Ango: Tun daga farkon tsayawar Jonathan suka zo suka same ni, na ce musu ni ba zan zabi Jonathan ba, a kan dalilai uku. Na farko shi ne ya kasa, bai iya shugabancin da ya wadata ba a Najeriya. Na biyu ba ya rike amana, kuma ba ya da alkawari. Na uku sabawar da ya yi na anihin cewa bai san da alkawari da aka yi da shi ba na cewa ba zai kara tsayawa zabe ba. Ka ga shi ma yana tare da wannan, to saboda haka a kan wadannan kawai ya nuna ba ya iyawa, kuma ba za a amince masa ba, ba ya rike alkawari saboda ba wai kawai don yana dan wata kabila ba ne, ko kuma daga Kudu yake ba. Na ce ni ba zan goyi bayansa ba, har ma sai da na kalubalance su na ce su kawo wani da suke ganin zai iya rike kasar nan su ga ko za mu raina. Amma wannan mun raina, to, balle ga amana wanda aka ci namu, kuma ga shi an kasa aiki. Haka shi kansa Obasanjo wanda ya tuntuba ya kawo shi tare da Umaru ai ya ga kasawar tasa ne ya sa ya rubuta masa wancan takarda. Obasanjo nasa laifuffukan kusan wadansu sun yi daidai da wanda Jonathan yake yi a yanzu, amma bambancinsu Obasanjo ya fi shi basira, ya kuma fi shi aiki, kuma koda aikin na shegantaka ne zai yi, to amma wannan ba ya iya komai ni a wurina.
Aminiya: To ga shi yanzu ana so mulkin ya dawo Arewa amma kuma wasunku sun fara rikicewa ko me ya kawo haka?
Farfesa Ango: To ai laifinmu ke nan mu ’yan Arewa, da ma laifin da ya kai mu ga halin da muke ciki ke nan Jonathan ke mulki. Wadannan da son kai wanda ba mu gada ba a wurin shugabaninmu na farko wanda suka rike mu har ma a wurin iyayenmu. Na rasa inda wadannan matasa suka gado wannan dan karen son kai da hadama, don shi ya kawo Jonathan yake mulki a yau. Ba don son kansu ba da hadama da maganar a ce Jonathan ya karbi mulki a shekarar 2011 bai taso ba. Saboda haka su din ne dai muke fama da su tun 2011 har yanzu da suka rage. Amma akwai wadansu daga cikinsu da yawa sun yi hankali sun dawo sun gane kuskuren da muke gaya musu, kuma sun same mu domin mu gyara. Don haka rashin hankali ne wani ya fandare daga wannan kokari da ake yi na ceto Najeriya, kuma za mu sa ido mu gani domin za mu gane su kwanan nan, inda za mu manna sunayensu, mu tabbatar da su suke yi, sannan su san cewa mun sani, mu san yadda za mu yi da su.
 Aminiya: To daga karshe wace shawara ke gare ka?
Farfesa Ango: To ba wani abin da ’yan Arewa za su yi su samu mafita daga wannan halin da take ciki illa ta hada kanta wuri guda, saboda da ma siyasar kasar nan haka take, ga nan ga can ga Kudu, kuma ga wane ga wane. To Malam Aminu Kano ya ce Najeriya babar kasuwa ce kowa ya ci da rana in dare ya yi kowa ya san gidan ubansa.