Zamu ci gaba ne daga inda muka tsaya makon da ta gabata akan Kalmar godiya,
Mun yi wani tambaya a karshen binciken mu cewa; Kana iya kara sakan daya ga rawuwan ka?
Babu shakka ansar mu zai zama ba wanda zai iya sai dai Allah mahalitcin mu, to idan fa haka ne, bamu da dalili da zai hana mu godiya ga Allah.
Mu duba rawuwan mu, zama cikin masu rai kadai ya isa mu nuna gadiyar mu ga Allah, lokuta da dama mukan manta da wannan, tunaninin mu yana kan yaya zamu yi Kudi, gidaje, motoci, tufa, nishadi, da dai sauransu, mukan manta da muhimman abubuwan da Allah yak e yi mana a kullayomi, mu tuna fa idan ba rai duk wadannan abubuwan banza ne.
Bari mu duba abin da Yesu Almasihu ya fada cikin littafin Matta sura shidda aya ashirin da biyar zuwa talatin da hudu (Matta 6:25-34)
“Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba? Ku dubi dai tsuntsaye, ai ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma tarawa a rumbuna, amma kuwa Ubanku na Sama na ci da su. Ashe ko ba ku fi martaba nesa ba? Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa? To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, duk da haka ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba. To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya! Don haka kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ ko, ‘Me za mu sha?’ ko kuwa, ‘Me za mu sa?’ Ai, al’ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka. Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa. Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe ta Allah ce. Wahalce-wahalcen yau ma sun isa wahala.” Ba za mu iya gane al’umuran Allah ba sai dai idan mun zama masu nuna godiya ga alheran Sa.
Gashi dai a kwana a tashi karshen shekara ta gabato, ya kamata mu yi nazari, bari mu kimanta ta daga rana ta fari cikin shekarannan zuwa ga rana ta yau, za ka iya irga albarkun da Allah ya baka? Albarkun na da dama fiye da yarda zamu iya tunawa ko kwatantawa, shi ya sa a littafin Afisawa sura biyar aya ta ashirin (Afisawa 5: 18) da kuma Tasalonikawa ta fari sura biyar aya goma sha takwas (1 Tasalonikawa 5:18) na cewa “Kullum ku riƙa gode wa Allah Uba da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a kan ko mene ne… “Ku yi godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu”. Bayan dalilai da muka bayar, yin godiya ga Allah na kara mana sanin girman Ubangiji Allah da kuma sannin ikon sa bisa rayuwarmu a kowane hali ta wurin Almasihu Yesu. Yin godiya kuma yakan kara karfin zumuncin mu da dogara ga Ubangiji ta wurin yin adu’a a ko da yaushe, a littafin Zabura ta sittin da takwas aya goma sha tara zuwa ashirin (Zabura 68:19-20) “Ku yabi Ubangiji, wanda yake ɗaukar nawayarmu ta yau da kullum, Shi ne Allah wanda ya cece mu. Allahnmu, Allah Mai ceto ne, Shi ne Ubangiji, Ubangijinmu, wanda yake cetonmu daga mutuwa” da kuma Kolosiyawa sura hudu aya biyu (Kolosiyawa 4:2) “Ku lazamci yin addu’a, kuna zaune a faɗake a kanta sosai, tare da gode wa Allah”.
A nan mun ga cewa yawan godiya ga Ubangiji na karfafa yin adu’a hakannan yawan yin adu’a kuma na karfafa yin godiya ga Allah, domin kafin mu mika bukatunmu ga Allah ta wurin yin adu’a, mukan fara ne da girmama Ubangiji Allah sannan mu gode Masa don kaunar Sa da yawan alheran da Yakan nuna mana a cikin rayuwar mu ta yau da kullum, kana mu mika bukatun mu gaba gare Sa don tabbacin abin da Ya ke yi a rayuwar mu a kullayomi.
Manzo Bulus ya bamu misali a Afisawa sura daya aya goma sha sidda (Afisawa 1: 16) ban fāsa gode wa Allah saboda ku ba, duk sa’ad da nake yi muku addu’a, haka kuma a wasikar sa ga Filimon sura daya aya uku zuwa hudu (Filimon 1:3-4) Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku, a kullum ina gode wa Allahna duk sa’ad da nake yi maka addu’a”. Wannan kadai ya isa mu sani cewa yin godiya ga Ubangiji ta wurin yin adu’a ma yana da mahimmanci kwarai da gaske.
Sai mu yi tunani, me zamu cewa Allah Ubangiji Mahalittcinmu, mai kula da mu, mai biyan bukatun mu, mai jin kukar mu, zamu yi ma Sa godiya ne ko kuwa gunanagunin cewa bamu sami abubuwan da ranmu ke bukata ba? Kada mu jira sai Ya kiraye mu, a kabari ba a shaidar godiya ko tuba, abin da kayi lokacin da kana raye, shi kadai zai fishe ka. Yin gunaguni da damuwa kan kudi, gidaje, sutura ko wasu kayan nishadi na duniya, baya hana mutuwa ba kuma baza mu iya tafiya da su ba, duk a nan duniya zamu barsu. To me yafi rayuwar shaidar godiya ga Allah?
Bari salamar Almasihu kuma ta mallaki zuciyarmu, domin lalle ga haka aka kira mu mu kuma kasance masu godiya ga Allah, sai kuma mun sadu mako mai zuwa da yard an Allah.