Abdullahi Dankama dalibi ne da ke ajin karshe a Jami’ar Bayero ta Kano, wanda ya fito da wani tsari da ba a saba gani ba, inda yake sayar da kayan marmari ta intanet tare da kai wa masu sayen kayan marmarin har kofar gidajensu.
A hirarsa da Aminiya ya bayyana yadda hakan ya bunkasa harkokinsa.
Yaya aka yi ka fara kasuwancin kayan marmari?
Na fara harkar sayar da kayan marmari a lokacin ina dalibi a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi.
Kasancewar makaranatar na kusa da ’Yan Lemo hakan ya ja ra’ayina na fara harkar.
To muna cikin yi ne sai Allah Ya kawo aka yi annobar cutar Kwarona wadda ta janyo hukumomi suka sa dokar zaman gida.
To a wannan lokaci sai ya zama mutane ba su samun abubuwan da suke so kamar yadda suka saba.
Kowa kuma ya san yadda ake bukatar kayan marmari a lokacin azumi.
Hakan ya sa na fara tallata kayan marmari a shafukana na sada zumunta, sai ga shi lamarin ya samu karbuwa a wajen mutane.
To dama mutane suna bukata, nan da nan sai mutane suka rika kirana suna gaya min abin da suke so.
Ni kuma sai in tura musu lambar asusun ajiyata na banki su tura min kudi a ciki sannan su ba ni adireshinsu. Ni kuma in kai musu har gida.
Daga baya sai mutane suka fara bukatar suna so su rika yin kyauta da kayan marmarin don haka sai na yi tunanin yin amfani da kwandon roba sai in shirya kayan yadda zai zama abin sha’awa ga mutane.
Sai na yi hoto na dora a shafukana sannan na ajiye wasu a nan wurin da nake sayar da kayan.
To hakan ba karamin birge mutane ya yi ba, shi ke nan sai mutane suka rika neman a shirya musu irin wannan kwandon.
Wasu ma ba a kasar nan suke ba, amma za su nemi in shirya musu kwandon don kai wa mutanen da suke so.
Wasu sukan nemi in kai wa mahaifansu, wasu shugabaninsu a wajen aiki, wasu kuma masoya ne ke neman a kai wa masoyansu.
Shi wannan kwandon ina yin sa hawa biyu akwai karami da muke sayar da shi Naira 6,000 sai babba da muke sayar da shi Naira dubu 10.
A wasu lokutan mukan ba mutum dama ya gaya mana irin kayan marmarin da yake so a hada masa a cikin kwandon.
Ban da wannan kuma akwai masu neman a shirya musu abin shan ruwa, to, irin wadannan mukan zauna mu yanyanka musu a zuba a cikin mazubin take-away a kai musu ya danganta da yawan mutanen da za su sha ruwan.
Wacce hanya kake bi wajen isar da kayan da aka nemi ka kai wurare daban-daban?
Gaskiya sakamakon bukatar da mutane ke yi na kayan marmari a wannan lokaci na azumi da yadda mutane suke bukatar a kai wa abokan arzikinsu kayan marmari ya sa na nemi masu taimaka min wajen gudanar da wannan aiki.
Kin ga na farko bayan ni da wani da muke sayar da kayan tare, ina da karin mutum biyu da suke kula da shirya min kwando.
Haka ina da masu babur mai kafa uku da suke kai kaya duk wurin da aka nema. Yawanci muna hada wa mai keke daya kayan unguwannin da ke kusa.
A rana musamman a farkon watan azumin nan mukan yi kwanduna sama da 50.
Wadanne kalubale kake fama da su a wannan kasuwanci?
Babban kalubalen da nake fuskanta shi ne kasancewar kayan maramari abubuwa ne da suke da lokaci, idan har wannan lokacin ya wuce to sukan lalace ko darajarsu ta ragu.
To irin wannan lokaci mukan fuskanci matsala idan mutum ya nemi mu kai masa kaya wani wuri, in muka je ya kasance bai san za a kawo ba, sai ki ga mun iske mutumin ba ya nan, Kwanan nan an kai kaya Sakkwato aka yi rashin sa’a ba ya nan.
Yanzu abin da muke yi shi ne idan muka iske mutum ba ya nan mukan nemi ya turo mana wakilinsa ya karba masa gudun kada su lalace.
Kamar kwana nan wani ya nemi mu kai wa wani abokin huldarsa kwando guda zuwa Kaduna, to sai bayan da aka je aka kira mutumin sai ya ce yana Abuja don haka sai ya turo matarsa ta zo ta karba a madadinsa.
Amma game da kudi na dauki matakai don haka ba ni da wata matsala.
Sai mun ga kudi sun shigo sannan muke aika kaya. Sai dai idan mutum abokin ciniki ne, to wannan da ya nemi a kai masa kaya za a kai masa ko ya biya ko bai biya ba.
Wane buri kake da shi game da kasuwancin kayan marmari nan gaba?
Ina da burin in ga cewa na samar da wani wuri da ake harkar shan kayan marmari kawai kamar yadda ake da wuraren da ake zuwa don shan fura ko ice cream da sauransu.
Ina so ya zama wannan wuri mun kawo kayan marmari mutum zai je ya sha.
Baya ga wanda za a yanyanka wa mutum a samu kuma wata na’ura da za a rika ,markada kayan marmari daban-daban ya danganta da wanda mutum yake so ya sha.
Idan Allah Ya yarda zan yi wannan nan ba da dadewa ba.
A yanzu ina ganin babu wani aiki da nake so fiye da wannan kasuwanci domin ina jin dadin yin sa.
Haka kuma alhamdulillah ina samu a ciki domin a yanzu na fi karfin mai albashin da za a rika biyansa Naira dubu 60 ko 70 a wata.
Wane kira kake da shi ga matasa ’yan uwanka?
Kullum sakona ga matasa shi ne su kama sana’a komai kankantarta. Mutum ya zama yana da wani tunani tare da kokarin sarrafa tunaninsa yadda zai dace da sana’ar da yake yi.
Idan kana kasuwanci ka rika kokarin kawo wani abu sabo da zai bambanta ka da masu kasuwanci irin naka.
Idan kin duba wajen nan mun kai mu takwas muke sayar da kayan marmari, to amma kasancewar na fito da wasu hanyoyi a yanzu ina samun ciniki sosai.