✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaman kotu ya gagara bayan Oshiomhole ya daukaka kara

Kotun daukaka kara a birnin tarayya Abuja ta gaza zama ta duba karar da shugaban jam’iyyar APC da aka dakatar, Adams Oshiomhole ya gabatar a…

Kotun daukaka kara a birnin tarayya Abuja ta gaza zama ta duba karar da shugaban jam’iyyar APC da aka dakatar, Adams Oshiomhole ya gabatar a gabanta.

Kwamitin kotun mai dauke da alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Stephen Adah, ta bayyana cewa kwamitin da ke da nauyin sauraron karar basu shirya ba.

Ba’a sa rana saboda sauraron karar ba, wanda Oshiomhole din ya shigar domin daukaka karar hukuncin da wata babbar kotun a Abuja ta yanke na dakatar da shi daga mukaminsa ba.

A karar da ya daukaka shugaban jam’iyyar ta APC din wanda aka dakatar ta hannun lauyansa, Damian Dodo ya yi nuni da cewa babbar kotun tayi kura-kurai a hukuncin da ta yanke.