Jagoran Kungiyar ’Yan Uwa Musulmi ta Najeriya (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya gana da wasu daga cikin ’yan Shi’ar da suka tsira yayin arangamarsu da sojoji a Zariya, Jihar Kaduna a shekararar 2015.
Ya kuma gana da iyalan wadanda suka mutu yayin arangamar.
- ’Yan sanda sun kama mutum biyu saboda fasakwaurin gasassun kaji
- Babu barazanar da za a yi mana kan ci gaba da mulki a 2023 – Dattawan Arewa
A ranar 28 ga watan Yulin 2021 ne Babbar Kotun Jihar Kaduna ta wanke Sheik Zakzaky da matarsa, Zeenat daga zarge-zargen da ake musu a kan laifuka takwas.
To sai dai da yake jawabi a Abuja, kamar yadda yake kunshe a cikin wata sanarwa da IMN ta fitar, malamin ya yi amfani da damar wajen jajanta wa wadanda lamarin ya shafa.
Ya kuma yi kira garesu da su tuna da irin musgunawar da Imam Hussein ya fuskanta lokacin da dakarun Yazidu suka hallaka shi.
Malamin ya kuma roki afuwarsu kan gayyato su da ya yi, maimakon shi ya je don jajanta musu.
“A sakamakon mummunar illar da aka yi mana lokacin da sojoji suka far mana, har yanzu muna dauke da burbushin albarusansu a jikinmu, hakan ne ya sa ba za mu iya haduwa da dukkan wadanda iftila’in na Disambar 2015 ya shafa ba,” inji shi.
Da yake mayar da martani, Dokta Waziri Gwantu, daya daga cikin masu ziyarar wanda ya ce ya rasa ’ya’yansa hudu a lokacin, ya nuna godiyarsa kan gayyatar, inda ya ce sun shiga mawuyacin hali a lokacin, inda ya jaddada cewa suna nan daram a kan akidar tasu.
Ita kuwa Hajiya Jummai Karofi, wacce ta rasa ’ya’ya biyar ta ce, “Ina so makasan ’ya’yana su san cewa abin da suka yi mana ba zai sa gwiwarmu ta sare ba daga yin biyayya ga Zakzaky da kuma Shi’a, a zahirin gaskiya ma, a shirye muke da mu yi amfani da jininmu wajen kare Musulunci.”