✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shirin da PSG da Bayern ke yi don zama Zakarun Turai

PSG na neman kafa tarihin cin kofin, Bayern Munich kuma rabonta da ci tun 2013

A ranar Lahadi 23 ga watan Agusta ne za a fafata wasan karshe na Gasar Zakarun Turai wato UEFA Champions League a filin wasa na Estádio do Sport Lisboa e Benfica da ke Portugal.

Wannan shi ne karo na farko da kungiyar PSG ta kai wasan karshe a gasar Zakarun Turai, ita kuma Bayern Munich tun shekarar 2013 rabonta da lashe kofin.

Ke nan PSG ba ta kofin ko daya, amma ita Bayern Munich tana da biyar.

Yadda PSG ta kawo wasan karshe

A wasanni 10 da suka buga zuwa wasan karshe, PSG ta lashe wasa 8, ta yi kunnen doki daya, ta rasa daya.

A wasa biyar na karshe da suka buga kuwa, sun ci hudu ne, suka yi kunnen doki a wasa daya.

Sannan ’yan wasanta guda biyu, Maurio Icardi da Kylian Mbappé ne suke gaba wajen zura kwallaye a gasar, inda suke da kwallo biyar-biyar.

Yadda Bayern Munich ta kawo wasan karshe

A nata bangaren, a wasanninta da ta buga guda 10, kungiyar Bayern Munich ta lashe duk guda 10 din, ciki har da ci takwas da ta yi wa Barcelona.

Sannan dan wasanta Robert Lewandoski shi ne kan gaba wajen zura kwallaye a gasar ta bana baki daya, inda ya zura kwallo 15.

Yanzu haka kwallo biyu yake nema ya kamo tarihin da Cristiano Ronaldo wanda ya fi zuwa kwallaye a gasar Zakarun Turai a kaka daya, inda Ronaldo ya zura kwallo 17 a kakar 2013-14 a lokacin yana kungiyar Real Madrid.

’Yan wasan da ake tunanin za su buga wasan

PSG: Rico, Kehrer, Thiago Silva, Kimpembe, Bernat, Paredes, Marquinhos, Herrera, Di María, Mbappé, Neymar.

Golan PSG na tunanin ba zai samu buga wasan ba, kasancewar yana fama da jinya; Sai Verati shi ma da wuya ya samu buga wasan na karshe.

Sannan kuma akwai rahoton da ke nuna cewa Neymar ya canja riga bayan wasansu na kusa da karshe da RB Leipzig, wanda ya saba dokar Covid-19, wanda ake tunanin za a iya dakatar da shi daga wasan na karshe.

Bayern Munich: Neuer, Kimmich, Boateng, Alaba, Davies, Goretzka, Thiago, Perišić, Müller, Gnabry; Lewandowski.

Wasanni a tsakinsu

Kungiyar PSG da Bayern Munich sun hadu sau takwas a gasar Zakarun Turai.

A wasannin, PSG ta doke Bayern Munich sau biyar, Bayern Munich ta lashe uku—ba su taba yin kunnen doki ba.

Wasan karshe na bana

A wasan karshen na bana, kusan ana tunanin cewa za a fafata matuka wajen kece raini tsakanin kungiyoyin guda biyu.

Ita dai PSG, ba ta taba lashe gasar ba, kuma ta dade tana neman lashe kofin.

Sannan attajirin dan kasuwa Tamim bin Hamad Al Thani na Qatar karkashin Qatar Sport Investment ya zuba jari matuka wajen sayen manyan ’yan wasa tun zuwansa.

Kudin da aka saya Neymer kadai wato Dala miliyan 263 wanda shi ne ya fi kowane dan kwallo tsada, ya isa ya sayi wani karamin kulob din.

Sannan albashinsa na Dala miliyan 350 a shekara ya isa a biya ’yan wasan wani karamin kulob din.

Bayan shi kuma ga su Mpape da sauran ’yan wasa masu tsada.

Ita kuwa Bayern Munich, tana da zaratan ’yan wasa ne da yawancinsu daga ’yan aro, sai wadanda ta saya da arha.

Daga cikin manyan ’yan wasan Bayern din, Robert Lewandoski kyauta suka dauko shi daga kungiyar Dortmund a shekarar 2014.

Muller a nan aka raine shi da sauransu da aka dauko a matsayin aro irinsu Coutinho da sauransu.

Akwai irinsu Alaba da a nan tauraronsa ya haska, da kuma Gnabry wanda tsohon dan wasan Arsnel ne da ya koma Werder Bremen daga can kuma ya koma Bayern.

Abin jira dai a gani shi ne: Shin PSG da ta dade tana kashe kudade domin lashe gasar Zakarun Turai za ta kai ga gaci; Ko kuma Bayern Munich ce da take da zaratan ’yan wasa, wadda ta yi kaca-kaca da Barcelone ce za ta lashe?

Hausawa na cewa rana ba ta karya.