A kwanakin baya ne hadin gwiwar kungiyoyin marubuta, wato kungiyar Marubuta Harsunan Gida Ta Najeriya (NILWA) da Dandalin Marubutan Jihar Katsina suka gudanar da taron bayar da kyaututtukan gasar rubutun gajerun labarai da da marubuci Rabi’u Na’auwa Balarabe ya shirya.
Taron wanda ya gudana a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa da ke Katsina, shi ne irinsa na farko da aka gudanar tun kafuwar kungiyoyin biyu.
An fara gudanar da taron da misalin karfe goma na safe, karkashin jagoranci Mukaddashin Shugaban jami’ar ta Umaru Musa, inda malami a Sashen Hausa, Dokta Bashir Abu-Sabe ya kasance mai gabatarwa.
A yayin gudanar da taron, an gabatar da makala mai taken ‘Illar Bangar Siyasa Ga Matasa, wadda Dokta Ahmad danmaigoro, malami a Kwalejin Ilimi Ta Tarayya da ke Katsina ya gabatar. Daga nan kuma sai mawaki Aminu Alan Waka ya shiga bajen kolin fasaharsa, inda ya yi wakoki da dama don nishadantar da mahalarta taron.
Marubuta kuma shugabannin kungiyar NILWA, Ado Ahmad Gidan Dabino da Malam Nasiru Wada Khalil suna daga cikin wadanda suka karanta bayanan zakarun da suka samu nasarar lashe gasar. Shi kuma Malam Muhammad Kabir, Shugaban kungiyar Marubuta Ta Najeriya Reshen Jihar Katsina da kuma Malam Aliyu Isa Funtuwa suka jagoranci raba kyaututtuka ga zakarun.
Zakarun da suka samu nasarar lashe gasar daga na daya har zuwa na hudu akwai sun hada da 1-Maryam Nuhu Turau da 2-Bello Hamisu Ida da 3-Muhammad Hafiz Koza Adamu da kuma 4-Fadila H. Aliyu Kurfi.
Wadanda suka dauki nauyin bayar da kyaututtuka a gasar sun hada da marubuci kuma Shugaban kungiyar Adabin Gargajiya Ta Najeriya (NFS), Dokta Bukar Usman OON da marubuci kuma memba a kungiyar NILWA, Malam Rabi’u Na’auwa Balarabe da kuma Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, a karkashin kamfaninsa na Gidan Dabino Publishers International.
Taron dai ya samu tagomashi daga manyan masana, wadanda suka samu damar halarta daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.
Zakarun gasar Adabi sun bayyana a Katsina
A kwanakin baya ne hadin gwiwar kungiyoyin marubuta, wato kungiyar Marubuta Harsunan Gida Ta Najeriya (NILWA) da Dandalin Marubutan Jihar Katsina suka gudanar da taron…