Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta sanar da sunayen ’yan kwallo 30 da za su fafata a gasar Gwarzon Dan Kwallon Afirka ta bana.
Hukumar ta sanar da sunayen ne a shafinta na Twitter a ranar Lahadin da ta wuce inda ta ce ta zakulo sunayen ’yan kwallon Afirka da ke wasa a sassan duniya su 30 ne don a tantance uku daga ciki wadanda za su fafata a gasar kafin ranar Talata 7 ga Janairun badi, inda za a bayyana wanda ya lashe gasar.
Daga cikin suunayen da CAF ta zakulo akwai wanda ya lashe gasar a bara Mohammed Salah dan kasar Masar da ke wasa a Liberpool da Sadio Mane dan Senegal da ke wasa a Liberpool na Ingila da Riyahd Mahrez wanda ya lashe gasar a 2016 dan Aljeriya da ke buga kwallo a Manchester City na Ingila da Odion Ighalo dan Najeriya da ke kwallo a China da Bictor Osinmhen dan Najeriya da ke wasa a kulob din Lille na Faransa da Wilfred Ndidi dan Najeriya da ke wasa a kulob din Leicester City na Ingila.
Haka kuma akwai Naby Kaita dan Guinea da ke wasa a Liberpool da Nicolas Pepe da Kwaddebuwa da ke wasa a kulob din Arsenal da sauransu.
Ana sa ran hukumar za ta bayyana wanda ya lashe gasar ce a ranar Talata 7 ga Janairun 2020 a bikin karrama ’yan wasan da zai gudana a kasar Masar.