✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zai yi wuya in fadi zabe mai zuwa – Buhari

Abin da ya sa ’yan Najeriya suke cikin talauci – Osinbajo   Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce zai yi wuya ya fadi a zaben…

Abin da ya sa ’yan Najeriya suke cikin talauci – Osinbajo

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce zai yi wuya ya fadi a zaben Shugaban Kasa da zai gudana a ranar 16 ga watan gobe.

Shugaban Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyi tare da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo a wani zauren tattaunawa da aka sa wa suna ’Yan Takara, a karkashin jagorancin fitacciyar ’yar jaridar nan Kadaria Ahmed.

Kadaria ta tambayi Shugaba Buhari ko zai amince da sakamakon zabe idan ya sha kaye? Sai ya amsa da cewa, “ina tunanin zai yi wuya in fadi.”

Shugaba Buhari ya kara da cewa, “Ina tunanin mun riga mun yi abin da za mu iya, kuma ina tunanin kin kalli gangamin yakin zabenmu na Bauchi da Kogi, sannan ki kokarta ki kalli sauran da za mu yi a sauran jihohin. Daga nan za ki gan ko zan samu nasara ko ba zan samu ba,” inji shi.

“Yadda mutune suka yi cincirindo a filin wasan da yadda na yi ta zagayawa ina ina yi musu bayanin yadda muka samu kasar lokacin da muka karbi mulki a shekarar 2015, da inda muke yanzu da nasarorin da muka samu a tsakanin shekarun nan, gaskiya na gamsu da yadda masu zaben suke na’am,” inji shi.

Bayan ya kammala jawabinsa ne sai jagorar shirin ta sake tambayarsa cewa, “duk da haka din dai, idan ka fadi zaben za ka amince da sakamakon zaben?”

Sai Buhari ya amsa da cewa, “ba zai kasance na farko da zan fadi zabe ba ai. Na gwada a shekarar 2003, inda na je kotu har na wata 30, a shekarar 20017 ma na je kotu na wata 18, haka kuma a shekarar 2011 na shiga kotu na wata 8, har na kai Kotun Koli. A karo na uku na ce Allah na nan, sannan a karo na hudu sai Allah da kuma kimiyyar zamani suka taimaka ta hanyar amfani da katin zabe na dindindin da na’aurar zabe. Kafin nan yadda suke yi kawai shi ne su zauna su rubuta sakamakon zaben da suke so, sannan su ce duk wanda bai amince ba ya kai kara kotu,” inji shi.

Ya ce “Yawancin masu zabena talakawa ne masu neman na abinci, ina suke da kudin zuwa kotu. Wannan ne ya sa suka mayar da al’amarinsu zuwa ga Allah, kuma Allah Ya amsa.”

A game da bidiyon Ganduje, Shugaba Buhari ya ce abin akwai mamaki matuka. Amma yanayin tsarin gwamnati ya kawo min sauki domin lamarin na gaban Majalisar Jihar Kano.

Sannan ya ce yana fata zai samu amsar da zai fada wa Kanawa daga kwamitin majalisar ko kotu kafin ya je Kano kamfe.

Shugaban Kasar ya ce duk da cewa har yanzu sojojin suna bukatar karin kayan aiki domin karasa murkushe Boko Haram, amma yana farin cikin ganin cewa yanzu mutane suna iya yin tafiya daga Maiduguri zuwa Kano a kan titi.

Sai ya bayyana cewa akwai wadanda suke tallafa wa Boko Haram daga kasashen waje.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce har yanzu ’yan Najeriya suna cikin talauci ne domin babu wanda ya dauki nauyin fitar da su daga talaucin.

Ya ce akwai lokacin da kasar nan ke sayar da gangan man fetur a kan Dala 100, inda kasar ta samu biliyoyin daloli, amma babu wani shiri da aka yin a fitar da mutane daga cikin talaucin da suke ciki

Osinbajo ya kara da cewa yanzu tattalin arzikin kasar ya habaka, ba kamar yadda suka same shi ba lokacin da suka karbi mulki.