✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zabukan Edo da Ondo: Babu takunkumi, babu kada kuri’a —INEC

INEC ta ce har yanzu da sauran aiki kan jefa kuri'a ta hanyar na'ura

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) Mahmood Yakubu ya ce dole ne masu kada kuri’a a zabukan gwamnonin jihohin Edo da Ondo su yi amfani da takunkumin kafin a ba su damar yin zabe.

Ya bayyana hakan ne yayin jawabin Kwamitin Kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da annobar COVID-19 a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce ya zama wajibi a yi amfani da kyallen don takaita kamuwa da kuma yada cutar tsakanin al’umma lokacin zabukan.

Shugaban hukumar ya kuma ce INEC za ta tabbatar masu zabe sun bayar da tazara tare kuma da samar da sinadarin tsaftace hannu a dukkan rumfunan zaben.

Kazalika, hukumar ta ja hankalin masu zaben kan tabawa ko jingina jikin kayan zaben, inda ta ce ba za ta lamunci hakan ba.

A kan batun amfani da na’ura wajen kada kuri’a kuwa, Farfesa Mahmud ya ce har yanzu akwai sauran jan aiki kasancewar doka ba ta kai ga amincewa da hakan ba.

Sai dai ya ce hukumar na sa ran amfani da su yayin zaben gwamnan Jihar Anambra da za a yi a shekarar 2021.

A wani labarin kuma, shugaban ya ce kwamitin na kar-ta-kwana ya ba da gudunmawar na’urar gwajin zafin jiki kimanin guda 3,000 ga hukumar wadanda za a kara a kan guda 1,000 da aka riga aka tanada kuma za a yi amfani da su yayin zaben jihohin biyu.