Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi watsi da rade-radin nada Shugaban Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Farfesa Eyitope Ogunbodede a matsayin Babban Baturen Zaben Gwamnan Jihar Ondo na ranar Asabar.
A safiyar Juma’a INEC ta ce bayanin Babban Baturen Zaben ya zama wajibi duk da cewa surutan ‘yan siyasa ba zai hana ta gudanar da aikita ba.
“Babban Baturen Zaben ba ma daga jami’ar yake ba kuma da dan Jihar Ondo ba ne”, inji Kwamishinan Wayar da Kai na hukumar, Festus Okoye.
Ya ce a ‘yan kwanakin da suka wuce ne INEC ta nada Babban Baturen Zaben kuma nan ba da jimawa ba zai gabatar da kansa ga Kwamishinan Zabe na Jihar ta Ondo a ranar da wasikar da aka ba shi ta ayyana.
Idan ba a manta ba, Gwamnan Ondo kuma dan takarar Gwamnan Jihar Ondo, karkashin jam’iyyar PDP, Seyi Makinde, a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana rashin amincewarsa da nadin Farfesa Eyitope Ogunbodede a matsayin baturen zaben.