Sakamakon zaben Gwamnan Jihar Ondo ya nuna Rotimi Akeredolu yana kan gaba a kananan hukumomi 12 cikin 15 da aka bayyana sakamakonsu.
Ya samu jimillar kuri’u 219,219 ga APC, yayin da abokin hamayyarsa Eyitayo Jegede na PDP ya samu 170,498.
- INEC na gab da sanar da sakamakon zaben Gwamnan Ondo
- Zaben Ondo: Akeredolu ya lashe kananan hukumomi 10
Ya zuwa yanzu dan takarar jam’iyyar ZLP (Zenith Labour Party), Agboola Ajayi, shi ne a matsayi na uku shi ne inda ya samu kuri’u 53,422.
An dakatar da sanar da sakamakon zaben a ranar Asabar bayan da aka bayyana sakamakon kananan hukumomi 12.
Da misalin karfe 9 na safiyar ranar Lahadi, an ci gaba da bayyana sakamakon inda Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta gabatar da na kananan hukumomi uku.
Ga dai sakamakon kananan hukumomi da ya zuwa yanzu Hukumar Zabe ta kasa ta fitar kamar haka:
Ose
APC: 15,122
PDP: 8,421
ZLP: 1083
Okitipupa
APC: 19,266
PDP: 10,367
ZLP: 10,120
Owo
APC: 35,957
PDP: 5,311
ZLP: 408
Ondo ta Gabas
APC: 6,486
PDP: 4,049
ZLP: 3,221
Akoko Ta Arewa maso Yamma
APC: 15,806
PDP:10,320
Akoko Ta Kudu maso Yamma
APC: 21,322
PDP:15,055
Akoko Ta Arewa maso Gabas
APC: 16,572
PDP: 8,380
Irele
APC: 12,643
PDP: 5,493
Ile Oluji
APC: 13,278
PDP: 9,231
ZLP: 1,971
Ifedore
APC:9,350
PDP:11,852
Akure Ta Arewa
APC: 9,546
PDP: 12,263
ZLP: 1,046
Idanre
APC: 11,286
PDP: 7,499
ZLP: 3,623
Ondo Ta Yamma:
APC: 15,977
PDP: 10,627
ZLP: 10,159
Odigbo
APC: 23,571
PDP: 9,485
ZLP: 6,540